✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yau Shugaba buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019

An girke jami’an tsaron DSS da ‘yan sanda a duk kofofin shiga zauren majalisar dokokin Najeriya, yayin da ake saran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai…

An girke jami’an tsaron DSS da ‘yan sanda a duk kofofin shiga zauren majalisar dokokin Najeriya, yayin da ake saran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 ga ‘yan majalisar dokokin kasar a yau Laraba.

Jami’an tsaron dai zasu yi kokarin dakatar da ma’aikatan majalisar da suke yin yajin aiki don yunkurin shiga zauren majalisar da shugaban kasar zai halarta.

Mai taimakawa shugaban Najeriya na musamman akan majalisar dattawa Sanata Ita Enang, ya tabbatar wa manema labarai cewa, shugaba Buhari a yau Laraba zai halarci zauren majalisar dokokin kasar don gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Ana saran kasafin kudin shekarar 2019 zai kai Naira tiriliyan 8.73.