Hukumar Yaki da Ayyukan Cin Hanci da Laifukan da Suka Danganci Almundahana ta ICPC, ta ce ta kammala shirye-shirye na gurfanar da Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda da a kwanannan ake zargi da kisan mijinta Bilyaminu Bello.
Hukumar ICPC jiya ta ce lokaci ya yi na gurfanar da Maimuna Aliyu, tsohuwar babbar jami’ar bankin ajiya da bayar da lamuni na Aso kuma dakatacciyar memba ta kwamitin gudanarwa ta hukumar ICPC.