✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yanzu Messi ne ya fi kowane dan kwallo daukar albashi

Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen, dan asalin Ajantina Lionel Messi ya shiga sgaban dan kwallon Real Madrid da ke Sifren Cristiano Ronaldo,…

Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen, dan asalin Ajantina Lionel Messi ya shiga sgaban dan kwallon Real Madrid da ke Sifren Cristiano Ronaldo, a wajen daukar albashi. A da Ronaldo ne yake sahun gaba, amma daga kakar wasanni ta bara zuwa ta bana, Messi ya sha gaban Ronaldo .

Kamar yadda kafar samar da bayanai ta daily mirrow da ke Ingila ta kalato ta nuna yanzu Messi yana daukar albashin da ya kai Fam miliyan 47 da dubu 800 a shekara wanda ya yi daidai dai Naira Biliyan 16 da miliyan 156 da dubu 400. Sai Ronaldo ya koma na biyu inda yake karbar albashin da ya kai Fam miliyan 39 da dubu 700 kwatankwacin Naira biliyan 13 da miliyan 418 da dubu 600. Sai na ukunsu Neymar da ke karbar albashin Fam miliyan 26 da dubu 800.
Sai dan kwallon PSG Thiago Silba da ke karbar albashin Fam miliyan 20.2 a shekara.
Robin ban Persie, dan kwallon Manchester United ne a matsayin na biyar inda yake karbar albashin da ya kai Fam miliyan 13 da kuma wasu alawus-alwasu da suka kai Fam miliyan 5 a shekara. Daga anan sai dan kwallon Real Madrid, Gareth Bale da ke karbar albashin da ya kai Fam miliyan 17 da dubu 500 sai kuma Wayne Rooneymai albashin Fam miliyan 16 da dubu 500.
Wadannan kudi da ’yan kwallon suke karba sun hada da na tsagwaron albashi da kuma tallace-tallacen da suka yi wa kamfanoni a sassan duniya.