✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A warware rikicin sarauta a tsakanin Banbare da Gumau – ’Yan Jihar Bauchi

Shugaban kungiyar ’yan asalin Jihar Bauchi mazauna Kuros Riba, Alhaji danlami Sale Rishi ya bukaci Gwamnatin Jihar Bauchi da masarautar jihar su warware takaddamar masarautar…

Shugaban kungiyar ’yan asalin Jihar Bauchi mazauna Kuros Riba, Alhaji danlami Sale Rishi ya bukaci Gwamnatin Jihar Bauchi da masarautar jihar su warware takaddamar masarautar Rishi, da ke karamar Hukumar Toro, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankalin wannan al’umma. Idan aka yi la’akari da rikicin sarauta da yanzu haka ya kunno kai tsakanin kabilar Banbare da kuma Gumau, lamarin da daga darajar wannna masarauta ya jawo yamutsa gashin baki tsakanin Banbare da mutanen Gumau .

Alhaji Sale Rishi ya bukaci haka tattaunawar su da Aminiya ya ce: “akwai wata masarauta ta gunduma da kabilar banbare, ke sarauta shi ne sai gwamnatin jiha ta yi kokarin fadadad masarautun jihar da ta yi, sai ta daga darajar gundumar Banbare zuwa ga masarautar hakimi, mai makon a nada maigundumar ya zama hakimi, sai aka dauko dan Sarkin Yakin Bauchi daga Gumau aka ba shi hakimi. Mutane na ganin ba a yi musu adalci ba,al’amarin ya haddasa bacin rai tsakanin gwamnati da wadan nan al’umma.”
Ya ci gaba da cewa kabilar Banbare sun shafe sama da shekara 100 suna sarautar wanna gunduma, amma an wayi gari a dauko wani ya zama hakiminsu tamkar ba a yi adalci ba, domin magance rigima da barnar dukiya “nake kira ga gwamnatin Jihar Bauchi da masarautar Mai martaba Sarkin Bauchi su duba lamarin nan da idon basira, su kawo karshen wannan takaddama.”
Alhaji danlami Sale Rishi ya ci gaba da cewa: “Su kuma wadanda suka shafe shekara sama da 100 suna wannan sarauta suka ga su fa ba a yi musu adalci ba, kamar yadda suka yi zargi sun kai kuka fadar gwamnati zuwa masarautar Bauchi da ma majalisar jiha, duk a cewarsu ba a yi wani abu akai ba, ya sanya nake kira gwamnati domin samun zaman lafiya kamata ya yi ta tsoma baki, gudun kada wani abu ya faru”.
A karshe shugaban al’ummar ya nemi gwamanti ta duba lamarin da idon basira, inda ya ce, yanzu zaman lafiya ake nema, musamman irin yadda matsalar tsaro ta addabi shiyyar Arewa maso Gabas, sai a yi kokarin warware waccan takaddama.