Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce’yan siyasa masu rike da madafun iko za a dora wa laifin gazawar Najeriya wajen samun wadataccen abinci.
Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wajen wata lacca da aka shirya domin bikin cikarsa shekara 86 a garin Abeokuta a Jihar Ogun.
Obasanjo, ya bayyana damuwarsa kan yadda Najeriya da Afirka suka kasa cin gajiyar ci gaban kimiyya da fasaha domin bunkasa fannin noma.
Ya roki ‘yan Najeriya da su zargi shugabannin kasar nan da rashin kishin wajen mayar da Najeriya jigon samar da abinci a Afirka.
Obasanjo ya ce, “Na yi imani Allah bai halicci Najeriya a matsayin kwando ba. Allah Ya halicci Najeriya da manufa mai girma. Najeriya tana da girman gaske.
“Don haka, ba Allah ne Ya jefa Najeriya cikin halin da ta ke ciki ba, mu ‘yan Najeriya ne muka jefa ta yanayin da ta ke ciki a yanzu.
“Amma, na yi imanin Najeriya ba za ta ci gaba da kasancewa a haka ba. Don haka, dole ne mu ci gaba da rike kanmu tare dagewa da yi wa kasa addu’a.”
A nasa jawabin, Darakta–Janar na Cibiyar Noma ta Kasa da Kasa (IITA), Dokta Nteranya Sanginga ya koka da cewa, kasashen Afirka duk da an albarkace su da su kasa mai albarka har yanzu tana kashe biliyoyin daloli wajen shigo da abinci.
Sanginga ya bayyana cewa, Najeriya na kashe Naira biliyan 11 a duk shekara wajen shigo da abinci cikin kasar nan.
Ya nanata cewa, dole ne Najeriya ta dogara da kanta wajen samar da abinci.