✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice…2

An sallami Rabiu Ibrahim daga asibiti bayan ya suma a lokacin da yake kwallo Tsohon dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Flying…

An sallami Rabiu Ibrahim daga asibiti bayan ya suma a lokacin da yake kwallo

Tsohon dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Flying Eagles Rabiu Ibrahim an sallame shi daga asibiti bayan ya fadi kasa sumamme a lokacin da yake wasa a gasar rukunin kasar Sukotlan (Scotland) a ranar Asabar da ta wuce.
dan kwallon ya suma ne bayan ya yi taho- mu- gama da  Darren Maatsen a farkon rabin lokaci a lokacin da wasa ke gudana.
Nan da nan aka dora shi a makara kuma aka garzaya da shi asibiti, amma har ya zuwa wannan lokaci ba a tantance musabbabin da ya sa dan kwallon ya suma ba.
Ana sa ran dan kwallon ya cigaba da wasa nan da ’yan kwanaki masu zuwa.

Ramsey ya ragargaji ’yan kwallon Arsenal

dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila Aaron Ramsey ya nuna bacin ransa a kan yadda takwarorinsa a kulob din suka bari kulob din Borussia Dortmund ya lallasa su da ci 2-1 a wasan zakarun kulob-kulob na Nahiyar da ya gudana a ranar Talatar da ta wuce.
Dortmund ta doke Arsenal ne da ci 2-1 a wasan.
dan kwallon gaba a Dortmund Robert Lewandoswski ne ya zura kwallo ta biyu ana gab da tashi wasan.
Ramsey ya yi nadamar ganin sun rasa maki uku a wasan duk da kokarin da suka yi.

Hamshakin dan kasuwa ya sayi kulob din Inter Milan

Shugaban kulob din Inter Milan da ke Italiya Massimo Moratti ya bayar da sanarwar shahararren dan kasuwar nan da ke kasar Indonesiya mai suna Erick Thohir ya sayi fiye da kashi saba’in na  hannayen jarin kulob din a karshen makon jiya.
A ranar Talatar da ta gabata ne Moratti ya tabbatar da wannan labari ga manema labarai a kofar shiga ofishinsa da ke Italiya.  Ya ce tuni suka kulla yarjejeniyar cinikin a tsakaninsa da shahararren dan kasuwar.
“Ina mai  farin cikin shaida muku cewa na sayar da fiye da rabin hannun jarin kulob din Inter Milan ga wani dan kasuwa mazaunin Indonesiya.  Na dade da yunkurin haka amma sai a wannan lokaci abin ya tabbata don haka nan gaba kadan zan sanar da duniya a hukumance”.
Ya zuwa wannan lokaci za a iya cewa akalla kashi saba’in na hannayen jarin kulob din Inter Milan ya zama mallakar Erick Thohir kenan.