Lionel Messi ba na sayarwa ba ne -Josep Maria
Sabon shugaban kulob din FC Barcelona da ke Sifen Josep Maria Bartmeu ya nanata kudurin kulob din na kin yarda ya sayar da shahararren dan kwallonsa Lionel Messi a kan kowane irin farashi.
Shugaban ya ce rahoton da ya bazu a duniya na cewa kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa yana yunkurin dauke dan wasan ko ta halin-ka-ka ba gaskiya ba ne.
Shugaban ya ce yana sa ran a ’yan kwanakin nan zai zauna da Messi don ganin ya sabunta kwantaraginsa a kulob din da hakan zai sa ya gama kwallonsa a Barca ba tare da ya canza sheka ba. Kuma tuni kulob din ya yanke shawarar kara wa Messi albashin da zai zarce kowane dan kwallo.
“Za mu zauna da mahaifin Messi don mu tattauna batutuwa a kan dansa Messi musamman abin da ya shafi kara wa’adin kwantaraginsa a FC Barcelona da hakan zai janye shakkun da wasu ke yi cewa ya kusa barin kulob din, inji Josep Maria a lokacin da yake hira da manema labarai.
Zaha da Fabio ’yan kwallon Manchester United sun koma Cardiff City
Yan kwallo biyu daga kulob din Manchester United da ke Ingila Wilfred Zaha da Fabio Da Silba sun canza sheka zuwa kulob din Cardiff City da ke Ingila.
Kocin kulob din Cardiff kuma tsohon dan kwallon United Ole Gunnar Solskjaer ne ya sanar da haka jim kadan bayan wasansu da United a ranar Talatar da ta wuce. A wasan, United ce ta doke Cardiff da ci 2-0
Ya ce an ba shi Zaha ne a matsayin aro zuwa karshen kakar wasa ta bana yayin da Fabio kuma ya kasnace ne a matsayin dan kwallonsu na dindindin.