Sergio Aguerro zai shafe mako takwas ba tare da yin kwallo ba
Shahararren dan kwallon kulob din Manchester City da ke Ingila Sergio Aguerro ya samu raunin da zai sa ya shafe makonni takwas ba tare da ya yi kwallo ba, kamar yadda kocin kulob din Manuel Pelligrini ya tabbatar a ranar Litinin da ta wuce.
Ageurro dai ya samu raunin ne a wasan da kulob din ya yi da na Arsenal a gasar rukunin Premier na Ingila bayan kulob din ya samu nasara a kan na Arsenal da ci 6-3 kuma Aguerro ne ya jefa kwallaye biyu daga cikin shida a raga.
Idan haka ta faru, Aguerro ba zai buga wasanni goma da kulob din zai yi ba ciki har da na gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai watau Champions League a wasan farko da kulob din zai yi da na FC Barcelona da ke Sifen a ranar 18 ga Fabrairun 2014 idan Allah Ya kaimu.
Ya zuwa yanzu Aguerro ya zura wa City kwallaye 19 a wasanni 20 da ya buga.
Liberpool ta fara yunkurin sabunta kwantaragin Luis Suarez
Kulob din Liberpool da ke Ingila ya fara yunkurin sabunta kwantaragin shahararren dan kwallonsa Lius Suarez don ganin ya hana shi canza sheka zuwa wani kulob.
Manajin Daraktan kulob din Mista Ian Ayre a ranar Talatar da ta wuce ya tafi Barcelona da ke Sifen don ganawa da wakilin dan kwallon mai suna Pere Guardiola a yunkurin sabunta kwantaragin nasa.
Luis Suarez ya so barin kulob din Liberpool a kakar wasan da ta wuce bayan kulob da dama ciki har da na Arsenal da ke Ingila da kuma na Real Madrid da ke Sifen suka yi zawarcinsa amma kulob din ya yi kememe ya ki sayar da shi.
Sai dai ya zuwa yanzu, Suarez yana tashe a kulob din na Liberpool musamman ganin yadda yake zura kwallaye a raga babu kakkautawa. Ya zura kwallaye 17 daga cikin wasanni 11 da ya yi wa kulob din a gasar rukunin Premier ta Ingila a bana da hakan ta sa ya zama dan kwallon da ya fi kowane yawan zura kwallaye a raga a gasar ta bana.
Luis Suarez, dan kimanin shekara 26 kulob din Liberpool ya sayo shi ne daga na Ajad da ke Holland a watan Janairun 2011 a kan Fam miliyan 22.8.