Doncaster zai dauke Macheda daga Manchester United
Kulob din Doncaster United da ke Ingila ya bayyana aniyarsa ta dauke dan wasan gaban kulob din Manchester United Federico Macheda ko da a matsayin aro ne. dan shekara 22 ya koma kulob din a matsayin aro ne a kakar wasan da ta wuce amma saboda raunin da ya samu ta sa har kwantaragin ya kare bai kara yi musu wasa ba don haka a wannan karo suke neman dauke shi a matsayin na dindindin idan ya samu sauki.
Kocin Arsenal da Aaron Ramsey sun lashe kyautar gasar Premier ta watan jiya
Kocin Arsenal, Arsene Wenger da kuma dan kwallon tsakiyarsa Aaron Ramsey sun lashe kyaututtuka daban-daban a gasar rukunin Premier na Ingila na watan jiya watau Satumba, 2013.
Yayin da Ramsey ya lashe kyautar dan kwallon da ya zura kwallaye hudu a raga a watan jiya bayan ya samu nasarar jefa kwallaye biyu ragar kulob din Tottenham sannan ya jefa daya a ragar Sunderland yayin da ya jefa kwallo daya a ragar Stoke da hakan ta sa ya hada kwallaye hudu a watan jiya (Satumba) shi kuwa koci Arsene Wenger ya lashe kyautar ce a matsayin kocin da ya fi kowane kokari a gasar a watan jiya.
Arsene Wenger da yanzu haka ya shafe kimanin shekara 17 yana horarwa a kulob din Arsenal, ya lashe kyautar sau goma sha uku kenan a tarihinta.
Wenger ya fara horarwa a kulob din Arsenal tun a shekarar 1996.
Ferguson zai koma ruwa
Tsohon golan kulob din Manchester United da ke Ingila Mark Bosnich ya ce ya fara tunanin shawo kan Sa Aled Ferguson, tsohon kocin kulob din don ganin ya janye ritayar da ya yi a karshen kakar wasan da ta wuce ya koma ruwa.
Sai dai ko da Ferguson ya janye ritayar ba zai koma yin koci a kulob din Manchster United ko kuma wani kulob daban a Nahiyar Turai ba sai dai ana sa ran zai zama koci ne ga kasar Austireliya a gasar cin kofin duniya da zai gudana a badi a kasar Brazil.