✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice…02

Tsohon dan kwallon kwando Micheal Jordan ya samu ’yan-biyu Tsohon dan kwallon kwandon Amurka Micheal Jordan tare da matarsa Ybette Prieto Allah Ya albarkace su…

Tsohon dan kwallon kwando Micheal Jordan ya samu ’yan-biyu

Tsohon dan kwallon kwandon Amurka Micheal Jordan tare da matarsa Ybette Prieto Allah Ya albarkace su da samun ’yan-biyun.
Matarsa mai suna Ybette Prieto ta haihu ne a ranar 9 ga watan nan da muke ciki a asibitin West Pam Beach da ke Florida, a Amurka.
Tuni mahaifan suka rada wa ’yan biyun da dukkansu mata ne sunan bictoria da kuma Ysable Jordan.
“Mahaifiyarsu tare da ’yan biyun suna cikin koshin lafiya”, kamar yadda mai magana da yawun iyalan Mista Estee Portnoy ya shaida haka ga manema labarai.
Wadannan ’yan-biyu sune ’ya’yan Micheal Jordan na farko tare da matarsa Ybette.  Amma Jordan mai kimanin shekara 50 ya haifi ’ya’ya uku tare da wata mata da suka hada da Jeffey dan shekara 24 da mace mai suna Jasmine ’yar shekara 19 da kuma Marcus James dan shekara 22.
A watan Afrilun bara ne Jordan ya auri Ybette mai kimanin shekara 34 ’yar asalin Cuba da ke zaune a Amurka bayan an gudanar da shagalin da aka dade ba a yi kamarsa a Amurka ba.

 

An nada shugabannin gudanarwar Kano Pillars

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da sanarwar rusa shugabannin gudanarwar kulob din Kano Pillars da ke karkashin shugabancin Malam Abba Yola.  Tuni gwamnatin ta  maye gurbinsu da sababbin shugabannin a karkashin jagorancin Akitek Ibrahim Haruna.
Mai ba Gwamnan Kano Shawara a kan Harkokin Wasanni Alhaji Ahmad Shu’aibu Gara ne ya sanar da haka ga manema labarai.
 Yadda tsofaffin shugabannin gudanarwar kulob din suka kasa ba marada kunya ta hanyar dora kulob din a turba ta gari ya sa gwamnatin yanke wannan shawara.  Alal misali an zargi tsofaffin shugabannin da laifin rashin samar da cikakkun bayanan yadda suke sarrafa kudin kulob din da rashin hadin kai a tsakaninsu al’amarin da ya sa kulob din ya fada matsala musamman a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Afirka watau CAF Champions League inda aka yi waje rod da Pillars tun a wasan farko.
Sababbin gudanarwar kulob din sun hada da Alhaji Garba Nuhu damburan a matsayin Mataimakin Shugaba yayin da Alhaji Aminu dan Amo da Alhaji Lawan Adda’u da Alhaji Sabo Abdullahi kofar Mata da Alhaji Bashir Mu’azu da Alhaji Naziru Aminu da Alhaji Kabiru Ali Dawaki da Alhaji Nasiru Garba Bichi da kuma Alhaji Garba Umar suke a matsayin membobi.
Tuni Gwamnan Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya amince da nadin da aka yi wa sababbin shugabannin gudanarwar kulob din na Pillars.