Iyalan wadanda aka sace a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun roki Gwamnati ta kara kaimi wajen ganin ta karbo ’yan uwansu da har yanzu ke hannun ’yan bindiga.
Wakilin iyalan Dokta AbdulFatai Jimoh, shi ne ya bayyana wa ’yan jarida hakan ranar Talata, in da ya ce lamarin ba karamin tashin hanakali ya jefa su ba.
A ranar 28 ga watan Maris din 2022 ce dai ’yan bindiga suka kai hari hadi da ta da bam a jirgin kasan yayin da yake tafiya, wanda ya yi sanadiyar mutuwa da jikkatar mutane da dama, hadi da garkuwa da wasu fasinjojin.
Jimoh ya ce wajen watanni biyu ke nan bayan sace fasinjojin amma har yanzu babu wani bayani kan kubutar da su.
“Lamarin ba karamin taba mu ya yi ba, wajen wata biyu ke nan da yin garkuwa da ’yan uwanmu, matanmu, ’ya’yanmu, kakanninmu, har ma da masu larura ta musamman da ke bukatar ganin likita a kai a kai.
“To ka kaddara halin da suke ciki a yanzu na firgici da tsoro, ga rana, ga damuna, babu wata kulawa, bakin ciki da damuwa kadai ya isa ya sanya musu larurar zuciya da kwakwalwa, da ma ta zahiri,” inji Jimoh.
Ya roku Gwamnatin Tarayya da dukkanin masu ruwa da tsaki da su yi abin da za su gani a kasa su karbo musu ’yan uwa.
Kazalika ya ce ’yan bindigar sun ce gwamnati ta san bukatunsu, don haka akwai bukatar gwamnati ta kawo karshen lamarin.
Ya kuma ce kamata ya yi ta dinga amfani da kafafen yada labarai wajen sanar da su halin da ake ciki dangane da wadanda aka sace din, kasancewar suna cikin yanayin damuwa.
Haka kuma, ya ce za su yi dukkan mai yiwuwa ta hanyar da ta kamata bisa doron doka domin ganin an fid da su daga mawuyacin halin da suke ciki.