✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A soma laluben watan Dhul-Hijjah daga ranar Laraba —Sarkin Musulmi

Sanarwar ta ce Laraba ita ce 29 ga watan Dhul-Qidah 1443 Bayan Hijirah.

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bukaci al’ummar Musulmi su soma laluben sabon watan Dhul-Hijjah daga ranar Laraba.

Sultan Abubakar ya yi wannan kira ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talatar nan ta hannun Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini na Fadar Sarkin Musulmin da ke Sakkwato.

Sanarwar ta ce Laraba ita ce 29 ga watan Dhul-Qidah 1443 Bayan Hijirah, kuma ita ce ranar soma duba sabon wata na Dhul-Hijjah 1443 Bayan Hijirah.

Ya kuma roki Allah ya taimaka wa al’ummar Musulmi wajen tafiyar da harkokin ibada a cikin sabon watan mai alfarma.

Dhul-Hijjah shi ne wata na 12 kuma na karshe a kalandar Musulunci da al’ummar Musulmi ke gudanar da Hajji da kuma bikin Sallah Babba – da ake gudanar da layya.