Majalisar Dattawa ta umarci Ma’aikatar Ilimi da ta assasa wayar da kan malam addini da masarautu kan matsalolin almajaranci.
‘Yan majalisar sun kuma bukaci a saka almajirai a matakin farko na karantun boko a Najeriya.
Sanatocin sun yi kiran ne yayin gabatar da rahoton kwamittin ilimi na majalissar, kan bukatar a saka almajirai a ckin tsarin ilimin matakin farko na Najeriya.
A bayaninta, Mataimakiyar Shugaban Kwamitin, Sanata Akon Eyakenyi, ta ce mafi yawancin almajirai a Arewacin Najeriya suke, kuma su ne mafi rinjaye a rashin zuwa makaranta da kuma yawan barace-barace.
Ta ce, ya kamata a yi amfani da damar da Gwamnatin Tarayya ta samar na dokar tilasta bai wa yara kanana ilimin boko a matakin farko, wato (Basic Education Act, 2004).
“Sai dai aiwatar da dokar ta UBEC Act, 2004 tana bukatar hadin kan gwamnatocin jihohi da amincewar majalisun dokoki na jiha”, inji ta.
Ta kuma ce Najeriya ta karbi bashin Dala Biliyan $611 hannun bankin duniya domin samar da ingantacen ilimi ga yaran da ba sa zuwa makaranta.