✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A sanar da al’umma idan akwai Coronavirus —Farfesa Idris

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar coronavirus na jihar Gombe Farfesa Idris Muhammad, ya bayyana cewa idan da gaske akwai cutar ta…

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar coronavirus na jihar Gombe Farfesa Idris Muhammad, ya bayyana cewa idan da gaske akwai cutar ta coronavirus ya kamata a ganota kafin ta yiwa jama’a illa.

Ya ce, nan da mako guda za’a samar da na’urar gwajin cutar a jihar wanda hakan zai kara sa a samu saukin gwaje-gwajen da sai an kai Abuja, amma samun na’urar zai sa a sake samun karuwar masu dauke da cutar sai dai kar hakan tasa mutane suji tsoro.

Shugaban ya ce yanzu daga bullar cutar zuwa yau sun yiwa mutane sama guda dari takwas gwaji a cikinsu ne aka samu guda 101 da suke dauke da cutar.

Farfesa Idris Muhammad, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa manema labarai karin bayani kan halin da ake ciki na cutar coronavirus a jihar, inda ya ce yanzu haka akwai masu cutar guda 101.

Ya ce, adadin da ake dasu duka ba ’yan asalin jihar bane wasu matafiya ne suka shigo da cutar amma sun yarda sun karbe su a hakan da yake suma ’yan Najeriya ne.

Game da boren da masu dauke da cutar suka yi a asibitin garin Kwadom inda aka killace su kuwa ya ce suna samun kulawar jami’an lafiya.

Sai dai ya ce abin da ya kara yawan masu dauke da cutar shi ne rashin samun hadin kan jami’an tsaro akan iyakokin jihar inda suke bari ake shiga da fita a lokacin da aka kafa dokar hana shiga ko fita a jihar, yayin da masu ababen hawa suke shiga ta cikin daji.

Farfesa Idris, ya kara da cewa, sun dauki alkawarin raba takunkumin fuska guda miliyan daya wanda za suka fara daga ranar Talata kuma za su tilasta mutane amfani da shi.