✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Sambisa zan tare idan na zama shugaban kasa —Al-Mustapha

Ya ce zai ba shugabannin sojoji wata shida su murkushe Boko Haram, idan suka kasa ya kore su, ya kuma bincike su

Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon Babban Dogarin Shugaban Najeriya na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, ya ce idan ya zama shugaban kasa zai tare a Dajin Sambisa na wata shida domin tabbatar da ganin sojoji sun murkushe kungiyar Boko Haram.

Al-Mustapha wanda ke neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar AA ya ce idan ya ci zabe, zai ba wa manyan hafsoshin tsaro wa’adin wata shida su murkushe kungiyar Boko Haram, idan sun kasa ya sallame su kuma ya hukunta su.

A cewar Al-Mustapha, “A wata shida a matsayina na shugaban kasa zan je Sambisa, can zan koma can zan yi hutu, zan yi hutun sati wurin in wani abu ya taba ni ma gani,” in ji shi.

Shegantakar nan ta Boko Haram ba, wallahi ni zan ce a wata shida in dai ba ta yi ba, duka manyan nan sai an rage muku girma, kuma za ku tafi gida, kuma za a hukunta ku, kudin da aka ba ku sai kun fid da shi, sai an yi musu bincike,” in ji shi.

A wata hira ta musamman da ya yi da Sashen Hausa na BBC, Manjo Al-Mustapha ya ce yana hawa mulki zai yi duk abin da ya wajaba a kansa na tabbatar da cewa cikin wata shida ya kawo karshen duk matsalolin tsaro da suka yi wa Najeriya katutu.

Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana takaicinsa kan yadda rashin tsaro ya yi wa Najeirya katutu, da kuma yadda ya ce sojojin kasar suka lalace ba su da kishin kasa da kuzarin da aka san su da shi a shekarun baya. 

A cewar tsohon hafsan sojin, a halin yanzu sojojin Najeriya sun koma ’yan sanda, kuma suna bukatar garambawul, su kuma ’yan sanda, lalacewarsu su ta kai matuka.

“Duk sojan Najeriya ni ina ganin shi daidai yake da dan-sanda na da, saboda sun riga sun zama dan sandan, kuma ’yan sandan da kuke da su sun gurbata, sun gurbata.”

A kan haka ne ya ce muddin ya hau mulki, dole a bi abin da ya tsara, “komai zafinsa a idon ko su waye”, musamman domin dawo da karfi da martabar sojojin Najeriya.

Ya bayyana cewa a cikin wata shida zai yi wa sojojin gagarumin garambawul mai zafi a wurin wasu, amma hakan ne zai dawo da martaba da karfinsu yadda aka san su a baya.

“Ni akwai abin da zan yi a wata shida, za ka ji tsoron abin da za a yi amma kuma shi ne gaskiya,” inji shi.

Dalilin takararsa

Ya bayyana takaicinsa kan tabarbarewar tsaro da ke addabar Najeriya da cewa lokaci ya yi da zai shiga siyasa ka’in da na’in.

Kamar yadda ya bayyaana, wasu kungiyoyi ne suka hada kudi suka saya mishi fom din takarar shugaban kasa, suka kuma ce ga jam’iyyar da zai yi takara.

Ya bayyana cewa ya ki shiga manyan jam’iyyun siyasa ne saboda yana ganin su ne suka lalata Najeriya.

Ya buga misali da cewa Shugaba Buhari mutum ne da suka sani tun suna kanana, ”Amma wadanda suka kewaye shi su ne gurbatattun Najeriya, suna nan da yawa.

“Yanzu in ka zauna ka ce ka dora wannan gwamnati a sikeli, ta’adin da suka yi ranar da zai fara fahimta, na san ranar zai sake tunani da yawa”.

Ya zargi gwmnatin Buhari da sakaci, musamman yadda shugaban kasar ba ya bibiyar abin da mutanen da ya damka wa amana suke yi.

Amma a cewar Al-Mustapha, idan ya shugabancin, shi da kansa zai nuna misali na bin doka, kuma ba zai sassautawa kowa ba, duk wanda ya saba doka, to za ta hau kansa.