✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A sake duba yiyuwar gina Kauyen Fina-Finai – Class Bei

Friday Abu da aka fi sani da Class B yana daga cikin mawakan Hausa na Hip-Pop a Jihar Kano a tattaunawarsa da Aminiya ya ce…

Friday Abu da aka fi sani da Class B yana daga cikin mawakan Hausa na Hip-Pop a Jihar Kano a tattaunawarsa da Aminiya ya ce yin kauyen fina-finai (Fim Billage) abu ne da zai kawo wa harkar fim da waka ci gaba domin za su yi amfani da wurin su samu saukin gudanar da lamuransu. Kuma a cewarsa wannan wuri zai haifar da hadin kai a tsakaninsu:

 

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?

Class Bei: Sunana Friday Abu amma an fi sanina da Class Bei a bangaren waka. An haife a Jihar Kaduna, na yi makarantar firamare a Kaduna. Daga nan muka dawo Kano da zama. A nan na yi karatun sakandare. Bayan na gama sai na samu shiga Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kano inda  na yi difloma a Harkokin Kasuwanci (Business Administration). Daga nan ban ci gaba da karatu ba sai na mayar da hankalina kan waka.

Aminiya: Yaya aka yi ka fara waka?

Class Bei: Eh, to na fara waka tun ina yaro domin a lokacin ban wuce shekara 10 da haihuwa ba. Na fara waka tun a Kaduna lokacin ina sauraron mawaka ina kwaikwayonsu. Idan mun je coci kuma ana dan ba mu dama muna nuna baiwar da Allah Ya ba mu. Bayan nan a unguwarmu akwai mawaka, ta haka ne na samu damar shiga harkar wakar Hip-hop sosai. Da na fara waka na samu goyon baya daga iyayena da ’yan uwana da abokan arziki. Kin san idan ana wakokin Hip-hop akan hada da rawa to duk da cewa na samu matsala a kafata daya amma hakan bai sanya na hakura da harkar ba.

Aminiya: Wakoki nawa ka yi kuma ka taba yin albam?

Class B: Gaskiya wakokin da na yi za su kai 20 ban da irin wadanda aka gayyace ni in yi wa baki a tarurruka daban-daban. Amma ban taba yin albam ba, amma a badi idan Allah Ya yarda zan yi albam guda 2.

Aminiya: Wace kungiyar mawaka kake ciki?

Class Bei: Gaskiya ba na cikin kowace kungiya sai dai ni ma na kirkiri wata kungiya wacce na yi mata lakabi da (NKE) ma’ana New Kings Entertainment wacce nake ganin za ta taimakaw a mawaka masu tasowa irina.

Aminiya: Ana zargin mawaka da rashin hadin kai me ke jawo haka, kuma yaya kake ganin za a gyara matsalar?

Class Bei: Wannan gaskiya ce, ana samun haka. Kuma ina ganin babu abin da ke kawo haka sai son zuciya. A ganina idan har ana so a dinke barakar da ke tsakanin mawaka to sai mawaka sun cire hassada da kushe, su sa son taimakon juna a duk lokacin da mai bukatar taimako yake bukatar wani tallafi.

Aminiya: Wane ne gwaninka a fagen waka wanda kake koyi da shi?

Class Bei: Gwanina a fannin waka shi ne Tekno kuma shi ne mudubina a harkar waka saboda ba ya da wani abu da zai yi bai burge ni ba.

Aminiya: Wane kira kake da shi ga mawaka ’yan uwanka?

Class Bei: Akwai bukatar mawaki ya zama mai rikon amana da fita daga cikin abin da ba ruwansa.  Haka kuma ya zama mai jajircewa sannan ya dauki sana’arsa da muhimmanci.

Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati?

Class Bei: Kiran da nake da shi ga gwamnati shi ne ta kara ba mu gudunmawa a kan wacce take ba mu, domin mawaki ba abin wasa ba ne, kasancewar muna tura sako ya isa inda ake so ya isa fiye da sauran kafafen tura sakonni. Gwamnati kanta tana amfani da mu idan tana so ta cimma wasu bukatu nata. Muna kara kira ga gwamnati ta sake kai korafinmu sama a kan maganar Film Billage, ma’ana a sake duba batun yiyuwar samar mana da wannan waje, don hakan zai sa mu kara samun sauki a harkokinmu  na yau da kullum kasancewar idan mutum zai dauki waka ko fim zai yi abin cikin sauki game da yanayi da kayan da yake bukata ba sai ya tafi wani wuri yana nema ba. Haka samun wannan waje zai sa a samu hadin kai a tsakaninmu, kasancewar za mu rika haduwa da junanmu a a wuri daya wanda yake bukatar taimako ta fusakar aikinsa a take zai samu taimakon da yake bukata ba  tare da wata matsala ba.