Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bukaci a asoke Hukumar Zaben Jihohi (SIECs).
Ya ce, mayar da ayyukansu ga hukumar zabe ta kasa (INEC) zai tabbatar da ’yanci na gaskiya da samar da sakamakon zaben kananan hukumomi mai inganci.
Fagbemi ya bayyana wa taron kasa kan kalubalen tsaro da shugabanci nagari a Najeriya a matakin kananan hukumomi, wanda majalisar wakilai ta shirya cewa, soke kwamishinonin zaben jihohi zai yi tasiri gami da ba da dama dimokuradiyya ta samu gindin zama a kananan hukumomi.
Hakan a cewarsa, zai kawar da duk matsalolin da ke kawo cikas ga cigaban kananan hukumomi da kuma iya gudanar da ayyukansu da tsarin mulki ya amince da su.
- ’Yan Sanda Sun Kama Sojoji 4 Kan Fashi Da Makami
- Buratai ya bukaci sojoji su gaggauta murkushe ’yan ta’addanci
“Don cimma wannan, masana da dama sun ba da shawarar cewa akwai bukatar a soke hukumar zaben jihohi.
“Ya kamata a mayar da ayyukansu da ikonsu ga hukumar INEC, saboda gwamnoni da dama na amfani da hukumar zaben jinharsu. Wannan shi ne ummul haba’isin matsalar shugabancin kananan hukumomi a Najeriya”.
Ya ce duk da tanade-tanaden da tsarin mulki ya yi na tabbatar da ’yancin kananan hukumomi, gwamnatocin jahohin na ci gaba ruguza su ba bisa ka’ida ba, suna kuma raba kansu.
Ya kara da cewa, asusun bai-ɗaya na jihohi da kananan hukumomi ne ya hana kananan hukumomin ci gaba tun jamhuriya ta hudu.