✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika taimakon ’yan sanda da bayanai – Kwamishina

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta gudanar da taro da sarakuna da fitattun mutane da kuma shugabannin kungiyoyin al’umma, inda ta nemi al’umma su rika…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta gudanar da taro da sarakuna da fitattun mutane da kuma shugabannin kungiyoyin al’umma, inda ta nemi al’umma su rika taimaka musu da bayanai game da wurare da kuma masu aikata laifuka.
Taron, an gudanar da shi ne a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin Kebbi, inda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ibrahim M. Kabir ya jagoranta.
Da yake yi wa jama’a jawabi a kan muhimmancin taron, Kwamishinan ya ce taron ya zama wajibi domin samun kariya ga jama’ar Jihar Kebbi da kuma cike gibin da ke tsakanin ’yan sanda da jama’a da kuma shigo da jama’a wajen dakile aikata manyan laifuffuka a cikin al’umma.
Ya ce aikin ’yan sanda yana da yawan gaske, a kan haka ne ya yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi su rika bai wa ’yan sanda bayanai da gaggawa a kan abin da ba su yarda da shi ba, domin sai jama’a sun taimaka musu da wasu bayanai, saboda ba komai ne  dan sanda ya sani ba; in ba an kawo musu rahoto ba irin abubuwan da ke faruwa a wasu wurare, saboda kawo dauki a cikin gaggawa.
Kwamishinan ya kuma jawo hankalin sarakuna da shugabannin al’umma su rika ilimantar da jama’a a kan aikin ’yan sanda da kuma muhimmancin aikin ga al’umma, inda ya kara da cewa dan sanda ba abokin gabar jama’a ba ne, ba ya iya gudanar da aikinsa dole sai da hadin kan al’umma da kuma goyon bayansu.
A karshe ya yi kira ga sarakunan da masu hannu da shuni da kungiyoyi, kan su rika taimaka wa rundunar ’yan sandan da kayan aiki da  na inganta rayuwa.