✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika hukunta masu yada jita jita a kafafen sada zumunta – Akibishop Kaigama

Bishop din Cocin Katolika na Jos kuma Shugaban Majalisar Bishop-Bishop din darikar Katolika ta Najeriya Akibishop Ignatius Kaigama ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan…

Bishop din Cocin Katolika na Jos kuma Shugaban Majalisar Bishop-Bishop din darikar Katolika ta Najeriya Akibishop Ignatius Kaigama ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta dauki matakin hukunta wadanda suke yada jita-jita a kafofin sada zumunta na Intanet a kasar nan. 

Akibishop Ignatius Kaigama ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da Aminiya kan hare-haren da masu fafutikar neman kasar Biafara suka kai wa ’yan Arewa mazauna Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a makon jiya.

Ya ce ya kamata gwamnati ta yi wani abu a kan masu yada jita jita a kafofin sada zumunta na Intanet, domin wadanda ba su da tunani da fatan halin alheri ga Najeriya suna amfani da kafofin wajen yada  abubuwan karya da suke tayar da hankalin jama’ar kasar nan.   

Akibishop Kaigama ya ce “Muna neman ci gaban Najeriya ne ko a Arewa ko a Kudu, muna neman ci gaba ne, amma wannan lamari da ya faru ba abu ne da zai taimaki kasar  nan ba.”  

Ya yi kira ga ’yan Najeriya su zauna lafiya su yi hakuri da juna.