✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika ba mawaka masu tasowa damar yin wasa – Swizz’ Jay

Jamilu Mikha’il Yahaya da ake kira Swizz’ Jay mawakin Hip-Hop da R&B ne, a tattaunawarsa da Aminiya ya koka kan yadda ba a ba mawaka…

Jamilu Mikha’il Yahaya da ake kira Swizz’ Jay mawakin Hip-Hop da R&B ne, a tattaunawarsa da Aminiya ya koka kan yadda ba a ba mawaka masu tasowa damar yin wasa da sauran batu:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Jamilu Mikha’il Yahaya. Ni dan asalin Jihar Kano ne amma a Jihar Kogi aka haife ni. Kuma na yi dukan rayuwata a Jihar Kano.Na yi karatun firamaren da sakandare a Unguwar Fanshekara. Bayan na kammala sai na tafi Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Bichi inda na samu takardar shaidar NCE. A yanzu haka bayan aikin koyarwa da nake yi a wata makarantar mai zaman kanta ina kuma yin sana’ar aski. 

Yaya aka yi ka fara waka?

Na fara waka tun ina firamare, lokacin wani yayana Mubarak yana yin waka, idan zai yi wakar yakan gayyace ni. A haka sai na fara sha’awar waka har na fara rubutawa sai dai a wancan lokaci ban kai ga bugawa ba sai da na shiga sakandare wajen shekarar 2010. Daga nan ne na fara haduwa da mawaka idan na je sutudiyo. Da haka tare da shawarwarin mawaka da ke sama da ni nake kara samun ci gaba, domin a yanzu har na samu damar yin wakoki da manyan mawaka kamar su Dokta Pio da Billy O da MK da sauransu. A yanzu haka ina da aiki da wadansu mawakan. 

A waka wane bangare kai ka fi yin wakokinka?

Ni dama mawakin Hip-Hop da R&B ne. Kuma yawancin wakokina na yi su ne a kan abin da ya shafi rayuwar al’umma. Haka ina yin wakokina a kan zaman lafiya kuma nakan yi a kan soyayya. Zuwa yanzu wakokina da na buga za su kai 20 sai dai bakwai daga cikinsu ne aka watsa su a blog inda mutane suke daukarsu ta Intanet. Kuma wasu wakokin nawa ana sanya su a gidajen rediyon Dala FM da Rahama Rediyo. Har zuwa yanzu ban taba yin albam ba, kodayake a yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa game da albam din da zan fitar a karshen shekarar nan ko farkon badi.

 Wane kalubale kake fuskanta?

Babban kalubalen da mawaka ke fuskanta shi ne rashin kudin buga waka a sutudiyo da yadda idan mutum ya je wani taro da mawaka za su yi wasa ba a ba shi dama, wai don shi sabon mawaki ne ko ba a san shi ba. Sai ka ga idan mawaki ba naci gare shi ba, to hakan sai ya kashe masa gwiwa.

A ganina idan ana ba mawaka masu tasowa damar yin wasa, hakan zai karfafa musu gwiwa sannan daga haka ne mutane za su san su a fagen waka. 

Kana da kira ga gwamnati?

Zan iya cewa gwamnati ba ta kula da mawaka, don ni a iya sanina ban san an taba samun wani taimako daga gwamnati ba. Ina ganin da gwamnati za a taimaka mana za mu fi haka, domin za mu iya yin kafada-da- kafada da ’yan uwanmu mawaka na wasu bangarorin. Akalla gwamnati ta zo ta ga ma me muke yi, sannan ta ga wane irin taimako za ta yi mana. 

Kana da kira ga ’yan uwanka mawaka?

Duk da cewa mawaka muna da kamfanoni daban- daban da muke yin wakokinmu, amma akwai hadin kai a tsakaninmu. Harkar waka abu ne da ke sa hadin kai ba wai yi wa juna hassada ba. Da zarar mawaki ya ji wakar dan uwansa mawaki sai ka ga yana kokari su hadu da juna, daga nan kuma za ka ga sun kulla abota har ma a wasu lokutan ya kai su yi waka tare.

-Ina kira ga mawaka su rika amfani da waka wajen isar da kyawawan sakonni da za su amfani al’umma. Al’umma ina kiran su daina kyamar mawaka, domin waka ba hanya ce ta lalacewa ba.