Saleh Tanko wanda aka fi sani da “Lalo” ya rasu ne bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya.
An yi shiru na kimanin minti daya a wasan da kungiyar kwallon kafa ta Kaduna United ta yi da kulob din Crown FC da ke Ibadan a gasar rukunin Premier na kasa don karrama marigayin kuma kulob din Crown ne ya samu nasara a wasan da ci 1-0.
Marigayi Saleh Tanko ya taba buga wa kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees da ke Kaduna wasa kuma ya buga kwallo a kungiyoyin kwallon kafa da dama a ciki da wajen Kaduna kafin daga bisani ya zama koci a kulob din Kaduna United.
Tuni Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa NPL ta aika da sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin da kulob din Kaduna United da kuma gwamnatin Jihar Kaduna bisa ga rashin Saleh Tanko da aka yi.
Haka shi ma Janar Manaja na kulob din Kaduna United Garba Lawal ya bayyana rashin koci Saleh Tanko a matsayin babban rashi ga kulob din da Jihar Kaduna da ma kasa baki daya. Ya ce rashin ba ga iyalan mamacin kadai ya tsaya ba, ya shafi kungiyar kwallon kafa ta Kaduna United da Jihar Kaduna da ma kasa baki daya. Daga nan sia yay i addu’ar Allah Ya gafarta wa mamacin, Ya kuma ba iyalansa hakurin wannan babban rashi da aka yi. Tuni aka yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A ranar Lahadin da ta wuce ne kocin kungiyar kwallon kafa ta Kaduna United Saleh Tanko ya rasu.
Saleh Tanko wanda aka fi sani da “Lalo” ya rasu ne bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya.An yi shiru na kimanin minti…