✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A magance cin zarafin malamai

Malamai na rayuwa cikin firgici, musamman a jihohin da aka rika kai musu hare-hare

Cin zarafin da dalibai da iyayensu ke yi wa malamai ya zama ruwan dare a kasar nan. Hakan ya sa malamai na rayuwa cikin firgici, musamman a jihohin da aka rika kai musu hare-hare.

Rahotanni daga kafafen labarai na nuna cewa, daliban da malaman makaranta suka hukunta saboda rashin da’a sukan shirya kansu don cin zarafin irin wadannan malamai.

Shigar da iyaye a cikin wannan lamari na rashin da’a da rashin mutunci yana kara dagula al’amuran.

A Jihar Ogun, misali, ’yan sanda a ranar 12 ga Oktoba, 2021, sun kama wani matashi mai shekara 35 mai suna Abidemi Oluwaseun, da laifin kutsawa cikin Kwalejin Baptist Girls College Idi-Aba da ke Abeokuta, tare da ’yan daba domin kai wa wani malami farmaki wanda suka zarga da dukan wata daliba mai shekara 15.

Malamin ya ladabtar da dalibar mai suna Oluwaseun da wadansu ta amfani da bulala sakamakon sun yi kokarin kawo wa darasinsa tangarda, suna yi masa ba’a da kuma raba hankalin sauran daliban.

Saboda fusata da abin da malamin ya yi, mahaifin dalibar ya dauki hayar wadansu mutum biyu suka kutsa cikin makarantar da wata mota da ba ta da rajista, dauke da makamai tare da yin barazanar sassara malamin.

Hukumomin Jami’ar Ilorin a ranar Talata, 16 ga Nuwamba, 2021, sun kori dalibin jami’ar Salaudeen Waliyullah Aanuoluwa da ke matakin karatu na 400 a Sashen Nazarin Halittu, bisa laifin lakada wa wata malama mai suna Misis Zakariyyah duka har ta suma.

An ce dalibin ya ci zarafin malamar tasa ce a kan rashin jituwa game da batun da ya shafi horarwar sanin makamar aiki (Students Industrial Working Edperience Scheme- SIWES).

Hakazalika, Gwamnatin Jihar Oyo a makon jiya ta dakatar da wata dalibar makarantar sakandare ta Jericho da ke Ibadan saboda ta jagoranci iyayenta da ’yan daba wajen lakada wa malamanta duka.

Na baya-bayan nan, wanda shi ne mafi muni zuwa yanzu, shi ne batun Ezeugo Joseph, wani malami a wata makaranta mai zaman kanta da ke Abraka a Jihar Delta, wanda ya rasu bayan da wadansu da ake zargi daga cikin dalibai sun yi masa duka a ranar Alhamis 2 ga Disamba, 2021.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Bright Edafe, ya ce wanda ake zargin mai suna Michael Ogbeise, dalibin ajin karshe na babbar sakandare (SS3), ya far wa malamin ne saboda ya yi wa kanwarsa Promise bulala.

DSP Edafe ya ce, malamin ya fadi a kasa bayan da wanda ake zargin ya lakada masa duka. An kai malamin asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Hadarin cin zarafin malaman jami’o’i da sakandare da wadanda ya kamata su girmama su ke yi, ya zama abin damuwa.

Makaranta tsari ne mai dauke da ka’idojin da ke jagorantar tarbiyyar dalibai da malamai; tare da kayyadaddun dokokin ladabtarwa don masu munanan halaye.

Ilimi ba kawai koyon karatu ba ne, har ma da koyon dabi’u.

Dole ne a gida ya zama ana kokarin yaba wa makarantun don koya wa yara dabi’u.

Koyon dabi’a ba motsa jiki ba ne a makaranta.

Iyaye masu tarbiyya wadanda suke da alhakin kula da dabi’un ’ya’yansu ba zai yiwu su je makaranta don cin zarafin malami ba.

Shigar da iyaye ke yi wajen dukan malaman ’ya’yansu, shi ne mafi munin rashin da’a, rashin kunya da muguwar dabi’a da ba a zata ba ga duk wani babba mai hankali da ya isa a kira shi mahaifi.

Wannan ba wai kawai nuna rashin mutunta malamai ne da al’umma ke yi ba, a’a yana kara nuna yadda dabi’u suka lalace musamman a matakin iyali.

Cin zarafin da dalibai ke yi wa malamansu na jefa makomar kasar nan cikin hadari.

Wannan labari marar dadi bai kamata a bar shi ya zama al’ada ba.

Idan ana so a magance wannan batu, dole ne a dauki tsauraran matakai don tunkarar yanayin da ke yin barazana ga fannin ilimin kasar nan da kuma makomarta.

Idan aka yi la’akari da girman laifin da aka aikata, matakin da makarantu ko gwamnatocin jihohi suke dauka na tunkarar daliban da ke cin zarafin malamansu ya kamata ya wuce dakatarwa da kora.

Ya kamata a gurfanar da irin wadannan dalibai da iyayensu a kotu a yanke musu hukunci, kamar yadda doka ta tanada, hukunci a irin wannan ya kamata ya hada da biyan diyya ga malaman da dalibai ko iyayensu suka ci zarafinsu.

Aminiya tana kira ga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta bude littafin da za a iya sanya sunayen masu cin zarafin malaman a kasa, don haramta wa dalibai da iyayen da aka samu da laifin cin zarafin malamai sake daukar su a wasu makarantu.

A yayin da muke kira ga makarantu su dukufa wajen tsarin manufarsu, zai yi kyau su tanadi takardar yarjejeniya da iyaye kan halayen ’ya’yansu a lokacin shiga makarantar.

Muna ba da shawarar a samar da jami’an tsaro a makarantun domin dakile cin zarafin malamai.