✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kawo wa Majalisa kasafin 2021 da wuri -Lawan

Majalisar Dattawa ta bukaci bangaren zartarwa da ya hanzarta aiki a kan kasafin kudin shekarar 2021 domin kammala aiki a kansa da wuri. Shugaba Majalisar…

Majalisar Dattawa ta bukaci bangaren zartarwa da ya hanzarta aiki a kan kasafin kudin shekarar 2021 domin kammala aiki a kansa da wuri.

Shugaba Majalisar Sanata Ahmada Lawan ya ce da hakan zai ba bangaren zartarwa zai samu gama aikin zuwa karshen watan Satumba domin mika wa Majalisar ta yi nata bangaren.

“Za mu tabbatar cewa sun samu dukkannin taimakon da suke nema musamman daga Majalisar Dattawa domin cimma wa’adin.

“Bangaren zartarwar kuma dage da aiki a kan kasafin 2021, mu kuma a shirye muke mu karbi daftarin a karshen watan Satumba mu kuma tabbatar an amince da shi kafin karshen watan Disamba”, inji shi.

Ahmad Lawan ya yi maganar ne bayan mika daftarin kasafin gajeren zango na shekarar 2021 zuwa 2023 ga kwamitocin Majalisar na kudi da tsare-tsare domin kammala aiki a kansa.

Shugaban Majalisar ya bukaci kwamitocin da za su mika rahotonsu bayan mako hudu, da su yi aiki da ma’aikatun kudi da tsare-tsare, su kuma taimaki hukumomin tara kudaden shiga domin samun nasara a ayyukan hukumomin.

A ranar Talata 21 ga watan Yuli ne Shugaba Buhari ya aike wa majalisar daftarin kasafin na gajeren zango domin fara aiki a akai.