✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karshe Gwamnatin Kaduna ta yi magana kan bacewar Dadiyata

Shekara daya bayan bacewar Abubakar Dadiyata wanda ya yi fice wajen sukar gwamnati

Gwamnatin Jihar Kaduna ta nesanta kanta da hannu a sace Abubakar Idris Usman, wanda aka fi sani da Dadiyata, wanda aka sace shekara guda a jihar kuma har yanzu babu labarinsa.

Shekara daya bayan bacewar tasa da ake zargin gwamnin jihar da hannu amma ba ta ce uffan ba, Ma’aikatar Sharia’arta ta ce Gwamnatin Jihar ba ta da masaniya ko hannu a bacewar Dadiyata wanda ya yi fice wajen sukar gwamnati.

“Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna na fada da babbar murya cewa Gwamantin Jihar Kaduna ba ta da masaniyar inda Abubakar Idris Usman wanda aka fi sani da Dadiyata yake ko hannu a bacewarsa.

“Duk wani tunani sabanin haka to kokari ne na cewa gwamnati na da hannu saboda a cikin Jihar Kaduna aka sace shi”, inji Kwamishinar Shari’a, Aisha Dikko.

Ta ce gwamnatin jihar ba ta taba kai korafin Dadiyata wurin ‘yan sanda ba ko kuma shigar da kararsa a gaban kotu.

A shekarar 2019 ne wasu ’yan bindiga suka dauke Abubakar wanda malami ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutisn Ma, a bayan ya dawo gidansa da ke a unguwar Barnawa, Kaduna da tsakar dare.

Tun daga lokacin ba a sake jin duriyarsa ko ganin motarsa da ’yan bindigar suka tafi da shi a cikinta ba.

Rahotanni sun ce Dadiyata na cikin yin waya ne bayan isowarsa gida kafin ya shida daki ’yan bindigar suka dauke shi da karfin tsiya suka sa a cikin motarsa sannan suka tafi da shi.

Sanarwar da kwamishinar ta fitar na martani ne ga korafin da ya kai ga janye gayyatar da aka yi wa Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai a matsayin mai jawabi a taron shekara-shekara na Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA).

Kungiyar ta soke gayyatar ne bayan wasu ’ya’yanta sun zargi Gwamna El-Rufai da tauye hakkin dan Adam da gazawa wajen magance kashe-kashe a Kudancin jiharsa da kuma da saba umarnin kotu na sakin mutanen da ke tsare.

Da take magana game da wadanda ke tsaren, Aisha Dikko ta ce dukkannin batutuwan da suka shafi manyan laifuka  “na kamanceceniya da juna wurin tunzura jama’a da yada bayanan karya da babu wata wayayyiyar al’umma da za ta lamunta, ballantana a jihar da ta sha fama da rikice-rikicen kabilanci da addini”.