Dan fafutukar nan na yankin Yarabawa, Sunday Adeyemi wanda aka fi sani da Igboho ya sake jagorantar wasu matasa wajen kone wani kauyen Fulani a Eggua dake yankin Yewa ta Arewa a jihar Ogun.
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Igbohon ya yi ikirarin cewa Gwamnan jihar ta Ogun, Dapo Abiodun ne ya gayyace shi domin ya taimaka masa wajen fatattakar makiyaya daga cikinta.
Wani mazaunin yankin, Alhaji Chede ya tabbatarwa da Aminiya cewa matasan sun sami nasarar kashe kaninsa, Jiji Danmawale sannan suka kone gawarsa.
“Yanzu haka muna yankin Randa na Abeokuta domin ganin mun sami gawar tasa don mu yi masa jana’iza.”
Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti-Allah ta Kasa reshen jihar Ogun, Alhaji Abubakar Ibrahim Dende ya tabbatarwa da Aminiya cewa Igboho da magoya bayansa sun cinna wuta a gidan sarkin Fulanin Eggua, Alhaji Abubakar Oloru.
Ya ce, “Sun kone gidan Sarkin Fulani Alhaji Abubakar Oloru wanda yake Eggua da yammacin ranar Litinin, sannan kuma da safiyar Talata suka kone kasuwar shanu ta yankin.”
‘Jami’an tsaro sun san da zuwansa’
“Mun yi ta kiran jami’an tsaro ciki har da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS saboda sun san da zuwansa, amma babu abinda suka yi.
“Mun ji labarin zuwansa ta gidajen rediyo kuma ance Gwamnatin jihar ce ma ta gayyace shi. Babu yadda muka iya, babu wanda zai taimake mu. Yawancin mutanenmu yanzu sun fantsama cikin dazuka,” inji shi.
Tuni dai jami’an ’yan sanda suka hallara a yankin na Eggua bayan faruwar lamarin.
Gwamnan Ogun ne ya gayyace ni in fatattake su daga jiharsa – Igboho
A ranar Litinin ne dai Igboho ya isa birnin Abeokuta na jihar ta Ogun inda ya ce Gwamnatin Jihar ce ta gayyace shi domin ya fatattaki makiyayan da suka addabeta da ma sauran yankin Yarabawa.
Ya dai sha alwashin karade dukkan jihohin yankin domin cika burin nasa.
A cewar Igboho, “Mun zo jihar Ogun ne domin mu fitar da makiyayan da suke kashe mutane.
“Ba mu ziyarci Gwamnan jihar ba sai mun kammala aikin da ya kawo mu tukunna, sai mun fatattaki Fulani makiyaya daga jihar.
“Ya kamata mu godewa Allah mu kuma yabawa Gwamnan saboda daukar wannan matakin, hakan ya nuna yana kaunar mutanen jiharsa.
“Da ba ya kaunarsu, da bai gayyace mu ba,” inji Igboho.
Sai dai Gwamna Abiodun ta bakin Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Waheed Odusile ya nesanta kanshi daga ikirarin na Igboho.
A wani labarin kuma, yanzu haka Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya fara wani taron tsaro da al’ummomin yankunan da lamarin ya shafa da nufin takaita bazuwar lamarin.
A ’yan kwanakin nan ne dai Igboho ya kai makamanciyar irin wannan ziyarar tare da kone gidan Sarkin Fulanin jihar Oyo dake Igangan, Alhaji Salihu Abdulkadir.