Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai su tabbatar an kare manoma a wannan lokaci na noma domin guje wa yunwa a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a hudubarsa ta Sallar Layy a ranar Talata.
“Mun gode wa Allah cewa ruwan sama ya fara sauka, duk da cewa, wasu sun ce ya makara amma haka Allah Ya so kuma muna godiya a gare shi.
“Yanzu lokaci ya yi da manoman mu za su koma gona, amma za su iya yin hakan ne kawai idan suka samu tabbacin tsaronsu.
“Don haka ina kira ga gwamnati a dukkan matakai da su tabbatar da tsaron lafiyar manoman su a gonakin su ko kuma kasar ta fada cikin yunwa,” inji Sarkin Musulmi.
Ya ce ana fama da tsananin wahala da yunwa a kasar, don haka ya bukaci shugabanni da su ji tsoron Allah su dauki matakai kan matsalolin.
Ya gargadi ’yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasar.
Ya bukace su da kada su gajiya wajen yi wa shugabanninmu addu’ar shiriya domin samun jagoranci mai kyau.
Ya yaba wa hukumomin tsaro kan abin da suke yi na maido da zaman lafiya a kasar.