Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta binciko, ta kama tare da hukunta wadanda suka wawure kayan tallafin COVID-19 a jihar a ranar Asabar.
Mataimakiyar Gwamnan jihar, Hadiza Balarabe a wata tattaunawarta da jama’ar jihar a ranar Lahadi ta ce tuni jami’an tsaro suka cafke wasu da ke da hannu a lamarin.
- #EndSARS: El-Rufai ya kara fadada dokar hana fita a Kaduna
- EndSARS: NECO ta dage ranakun jarabawarta
- Dokar hana fita ta koma sa’a 24 a Taraba
Balarabe ta ce, “Babu wani suna da za a iya kiran yadda ake wawure kayan tallafin COVID-19 face sata.
Mun tattauna da shugabannin al’umma mun kuma sanar da su cewa ba za mu lamunci abin da ya faru ba domin babu wani uzuri na aika manyan laifuka.
“Hakki ne a kan jihar ta nemo tare da hukunta wadanda ke da hannu cikin aikata laifin.
“Domin mu kare hakkin ‘yan kasa na gari, ba za mu bari masu ganin sun fi karfin doka sun rika abin da suka ga dama ba.
“Wadanda suka tunzura su da wadanda ke yada kalaman nuna tsana su ma su dakaci abin lokacin da doka za ta hau kansu”, inji Mataimakiyar Gwamnan.
Ta ce “wasushe yawancin kayan zai haifar da barazana ga lafiyar jama’a, saboda an debe lalatattun magungunan da masu hadari a ofishin hukumar NAFDAC da kuma tan 8,000 na waken soya da aka mai dauke da sunadari mai hadari da aka kwashe a wani kamfanin sarrafa abinci mai zaman kansa”.
Ta yaba wa jami’an tsaro kan dakile yaduwar tashin hankali kuma da cafke wasu daga cikin wadanda ke da hannu a cikin satar.
“Ina kira ga jama’ar Jihar Kaduna da su bi doka da oda kuma su ba jami’an tsaro hadin kai yayin da suke aiwatar da dokar hana fita.
Muna rokon ‘yan kasa da su sa ido sosai saboda rahotannin tsaro sun nuna cewa mutanen da ke neman zubar da jini na ci gaba da neman hanyoyin da za su wargaza jihar, ta hanyar amfani da jita-jita da labaran karya.
“Muna kira ga sarakuna, shugabannin al’umma da na addinai da su taimaka wa jami’an tsaro don fatattakar masu aikata laifuffukan da ke da hannu cikin mummunan abin da ke faruwa”, inji ta.
Ta kara da cewa an sanya dokar hana fita ta awa 24 a jihar ne don hana masu yin zagon kasa ga doka da jefa rayuka da dukiyoyin jama’a cikin hadari.