✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanatocin Arewa sun nemi a janye kudurin dokar harajin Tinubu

Sanatocin Arewa sun nemi a janye sabbin kudurorin dokar harajin da Tinubu ya mika wa majalisar

Sanatoci daga yankin Arewa sun bukaci a majalisar ta dakatar da aiki kan sabbin kudurorin harajin masu cike da rudani wanda majalisar ta kammala karatun farko a kansa.

Sun nemi hakan ne bayan wani zama a ranar Litinin, ida suka bayyana cewa kudurorin dokar na dauke da wasu tanade-tanade da ke barazanar talauta yankin Arewa.

Sanata Buba Umaru Shehu ya sanar cewa sanatocin Arewa daga duk jam’iyyu sun bukaci sun yi ittifakin cewa a dakatar da duk wani aiki a kan  kudurorin hudu masu cike da rudani.

Dan majalisar ya ce “Kudurorin na da sarkakiya don haka akai bukatar masana dokokin haraji su yi masa karatu a tsanake,” saboda rashin yin kyakkyawan nazari kan lamarin zai haifar da mummunar illa a nan gaba.

Sanata Buba, wanda ya soki yadda ake gaggawar aiki a kan kudurorin cikin ’yan kwanaki kalilan, ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa ba su amince da tanadin kudurorin game da tsarin rabon harajin sayen kayayyaki (VAT) ba, saboda sun lura cewa yankin Arewa zai cutu.

Sun cim-ma wannan matsaya ne bayan a karshen mako Majalisar Wakilai ta sanar da dakatar da tattawa kan kudurorin dokokin harajin da ke ta shan suka da jawo muhawara, tun bayan da Shugaban Kasa Bola inubu ya gabatar da su.

A nasa bangaren, Sanata Ali Ndume, ya ce zaman da sanatocin Arewa suka yi da gwamnoni da sauran shugabannin yankin, ya amince a janye kudurorin, a fadada tuntuba da neman shawarwari a kansu.

Ndume ya bayyana fatan gabatar da kudurinsu na neman janye batun dokokin harajin a gaban majalisar dattawa a ranar Laraba.

A cewarsa, matakin nasu ya yi daidai da shawarar majalisasr tattalin arziki ta kasa da majalisar sarakuna, kuma nan gaba majalisun dokokin jihohin Arewa za su sanar da adawarsu ga kuduurorin.

Dan majalisar ya kuma yi nuni da cewa wasu tanade-tanaden kudurorin harajin sun ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya don haka babu yadda za a yi aiki da su.

Idan an tuna, bayan kammala karatun farko, Majalisar Dattawa ta tura kudurorin ga kwamitin kudade domin nazarin sa, kafin daga bisani su gabatar da shi domin jin ta bakin jama’ar kasa da kuma kwararru.

Masu sukan kuduorin da suka hada da gwamnoni da sarakuna da ’yan majalisa daga yankin Arewa sun jima da neman shugaban kasan ya janye kudurin nasa, ya bari a fadada tuntuba da jin ra’ayoyin jama’a a kai, amma ya nemi majalisa ta ci gaba da aiki a kai.

Kungiyar gammayar ’yan Arewa (CNG) ta bakin shugabanta, Jamilu Charanchi, ta yi zargin cewa dokar za ta kara jefa al’ummar Arewa cikin karin kunci, baya ga wanda suke fama da shi na talauci da yunwa da rashin aikin yi da suaransu.

Shugaban kasa dai ya bukaci Ma’aikatar Shari’a ta yi aiki tare da Majalisa da sauran masu ruwa da tsaki domin yin gyare-gyare da inda aka gano matsaloli a kudurorin dokar.

Da yake tsokaci kan lamarin, ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa wasu abubuwan da ake yadawa musamman zargin neman talauta Arewa, ba sa cikin kudurorin, yana mai kira ga masu bayyana ra’ayi kan lamarin da su yi adalci kuma cikin mutunta juna.