✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A janye dokar ta-baci a Arewa maso Gabas

Dokar ta-baci da aka kakaba wa jihohin Adamawa da Barno da Yobe na tsawon wata shida za ta kare a ranar 12 ga Mayu, idan…

Dokar ta-baci da aka kakaba wa jihohin Adamawa da Barno da Yobe na tsawon wata shida za ta kare a ranar 12 ga Mayu, idan aka hada da wadda Shugaba Jonathan ya kakaba wa jihohin a ranar 20 ga Mayun bara, kuma ta kare a Nuwambar 2013. Jihohin uku sun kasance karkashin dokar na tsawon shekara guda. Ra’ayi ya bambanta kan matsayin dokar, inda aka yi kira kan ci gabanta ko kuma janye ta, al’amarin da aka fi yin karaji a kansa. Gwamnatocin jihohin da makwabtansu da daukacin Arewa sun bukaci a janye ta, yayin da wasu ’yan tsirari, wadanda mafi yawansu kungiyoyin addini ne da shugabannin kabilu daga Kudu, ke kafa hujja da tashe-tashen hankula, al’amarin da suka danganta kan kunar-bakin-wake, don haka suke bukatar ci gabanta.
A tsawon wa’adin matakan dokar da aka dauka, hare-haren kunar-bakin-wake sai karuwa suke yi, inda aka kona garuruwa da kauyuka. ’Yan Boko Haram sun yi ta kai hare-haren kan-mai-uwa-da-wabi, inda suka yi fata-fata da rayuka da dukiyoyi a daukacin fadin Arewa maso Gabas. Duk an aiwatar da wannan ne a gaban wadanda aka dora wa alhakin bayar da kariyar tsaro. Wani abin takaicin shi ne, masu son ci gaban dokar da masu son a janye ta, sun tabbatar da rincabewa harkokin tsaro, ta yadda za su san matsayin ra’ayinsu. Wadanda ke son dokar ta-baci, to ta kasa shawo kan harin kunar-bakin-wake, domin hare-haren da suka sassauta, sun kara kaimi. Su kuwa daya bangaren na nuni da cewa ruruwar wutar hare-haren don haka suke son dokar ta ci gaba.
A tattaunawa ta fahimta, a iya cewa kowane bangare na da manufa tagari ga wannan yanki, don haka suke son al’amura su saisaita, ta yadda za a samu kyautatuwar zamantakewa da damawar tatttalin arziki a kasar nan. Magana ta gaskiya idan aka yi la’akari da tasirin dokar ta-baci, za a ga cewa an tsawaita ta, kuma ta saba wa tanade-tanaden ’yancin dan Adam da dimokuradiyya, al’amuran da ake kokarin tabbatar da su a kasar nan. A halin yanzu, duk da cewa dole ne a shawo kan hare-haren, ko masu tsattsauran ra’ayi kan dokar, za su fahimci cewa, za a iya karya lagon kunar bakin waken ne, fiye da amfani da karfin soja da makamai. Akwai bukatar  amfani da makamai kamar yadda ake yi, amma abu mafi muhimmanci shi ne, ta hanyoyin lalama, wato shawo kan matasa a daina amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake, sannan a yi kokarin hana wadanda suka tsunduma cikin harkokin tada zaune tsaye.
Dabarun karya lagon hare-haren kunar bakin wake sun hada da jawo daukacin mutanen yankin Arewa maso Gabas a jika. Wannan ba aiki ba ne mai sauki, a irin wannan matsanancin yanayi a karkashin dokar tabaci, wadda tsananin tanade-tanadenta sun haifar da kiyayyar mutane ga sojoji, har ta ki ga ana bijiro da tambaya wadanne dokoki aka ba su umarni a kai. Don haka bai kamata a ci gaba da wannan doka da zarar wa’adinta ya kare.
Duk da bukatar janye dokar, wannan ba yana nufin a janye sojoji nan take ba; rikici ba zai sake rincabewa ba, matukar aka bi lalama da niyya tagari, ba tare da sanya siyasa ba, to za a iya shawo kan lamarin. Idan aka kara inganta harkokin tsaro a tsakanin fararen hula, sai a dauki sauran matakan da suka dace ta hanyar amfani da karfin soja, kuma wannan zai hada da shiga tattaunawar neman sasanci, don tabbatar da zaman lafiya. Abin farin ciki shi ne, an bullo da amfani da dabarun gargajiya a karkashin kulawar ofishin Shehun Barno da sauran sarakunan gargajiya, wadanda kimar darajarsu ke da matukar tasiri a cikin al’ummominsu.
A daukacin fadin Najeriya, babu yankin daba shi da dabarun warware matsaloli na gargajiya. Don haka lokaci ya yi da al’ummomin Arewa maso Gabas za su duba yiwuwar kara kaimi wajen karya lagon harin kunar bakin wake; Yawan cusa siyasa a irin wannan yanayi, ba zai gamsar ba, wajen kafa hujjar tsawaita dokar tabaci a wadannan jihohi uku.