✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A hukunta wadanda suka yi wa Fulani kisan gilla a Kaduna

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, Alhaji Kiruwa Ardon Zuru ya nuna damuwarsa kan rashin gurfanar da masu kashe Fulani a jihohin Kaduna da Zamfara,…

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, Alhaji Kiruwa Ardon Zuru ya nuna damuwarsa kan rashin gurfanar da masu kashe Fulani a jihohin Kaduna da Zamfara, inda kuma ya  nuna damuwa kan rashin kawo karshen kisan gillar da ake yi wa Fulani a kauyukan yankin Kajuru da ke Jihar Kaduna.

Shugaba Kiruwa ya bayyana hakan ne yayin da ya gudanar da taron manema labarai a Birnin Kebbi. Ya ce, “A kwanakin nan na tunatar da dukan hukumomin tsaron da ke da alaka da abin da ya faru a Kajuru da kuma tabbatar da cewa sun dauki matakin tabbatar da an kamo mutanen da suka gudanar da wannan kisan gillar ga Fulani mata da maza a yankin Kajuru a Jihar Kaduna, amma har zuwa yanzu da nake magana da ku, ba a iya kammala bincike game da kisan gillar da aka yi a yankin Kajuru ba balle a gurfanar da masu hannu a gaban kotu.”

Ya kara da cewa “Idan ba a kama masu laifi an gurfanar da su a gaban kotu ba,  hakan zai bai wa wadansu batagari damar aikata irin wadannan miyagun laifufukka a sauran jihohin kasar nan a karshe ya zama fadan kabilanci a tsakanin mutanen Najeriya.”

Saboda haka ya yi kira da babbar murya ga hukumomin da ke da hakki kan irin wadanan matsaloli su tabbatar sun gudanar da ayyukkansu ba sani ba sabo, don dakile masu iya tasowa a nan gaba.

Ya ce “An kashe Fulani a yankin Kajuru, da suka hada da yara mata da maza da matasa, kuma aka cinna wa gidajensu wuta kuma aka kashe musu shanu na miliyoyin Naira da kuma sace wasu shanun nasu. Don haka ne nake kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da kuma ta Gwamnatin Tarayya a taimaka wurin ganin an magance irin wadanan matsaloli masu tasowa a tsakanin Fulani da sauran jama’ar kasar nan, domin dukkanmu ’yan kasa ne ba tare da wani bambanci ba.”

Ya bukaci dukkan Fulanin kasar nan su ci gaba da zama masu bin doka da oda da biyayya ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi don a samu zaman lafiya.

Ya yaba wa al’ummar Fulanin kasar nan kan fitowa da suka yi don kada kuri’a a zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a kwanakin baya, wanda ya bai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari damar zama Shugaban Kasa karo na biyu. Kuma ya gode musu kan kasancewa masu hakuri bisa abubuwan da ke faruwa da su a kasar nan. Ya tabbatar wa jama’ar Fulani cewa “Nan ba da jimawa ba wadannan matsaloli za su kare, domin Kungiyar Miyetti Allah na iya kokarinta don ganin cewa an magance su,” inji shi.

A karshe ya kara jan kunnuwan al’ummar Fulanin kasar nan da sauran al’umma kan su yi hukurin zama da juna domin wanzar da zaman lafiya a Najeriya.