Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ya yi kira da a kamo tare da hukunta duk wadanda aka samu da lafin kona ofisoshinta kafin babban zaben 2023.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja a yayin taron tsaro na gaggawa babban ofishin hukumar a ranar Juma’a.
- An kai hari 47 kan ofisoshin INEC a shekara 3
- DAGA LARABA: “Mun Ci Karfin Aikin Zaben 2023” – Shugaban INEC
“Wannan hukuma ta damu sosai kan yawan hare-haren da ake kaiwa, ya kamata a kama da kuma dauki kwakkwaran mataki na hukunci (kan masu laifin) yayin da muke tunkarar zabe,” in ji shugaban INEC.
Ya ce, hukumar na daukar matakan gaggawa na gyara ofisoshin nata da aka kona, ta yadda za a fara amfani da su.
Taron gaggawan na zuwa ne bayan da aka kone ofishin hukumar da ke jihohin Ogun da Osun a ranar Alhamis, a inda aka kone sama da katunan zabe 65,000 da wasu kayyaki.