✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana fama da ƙarancin jami’ai a hukumomin tsaron Nijeriya — Lagbaja

Jami’an tsaro miliyan 2 ba za su iya tsare al’ummar Nijeriya fiye da mutum miliyan 200 ba.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bayyana damuwar cewa ana fama da ƙarancin jami’ai a hukumomin tsaron Nijeriya.

Lagbaja ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron lakca kan mutumin da ya fi fice a shekarar 2024 mai taken, “rawa da gudunmawar rundunar sojin Nijeriya ga ci gaban ƙasa”, wacce Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya da Muhimman Fannonin Ilimi, na Jami’ar Ilori ta shirya.

Ya buƙaci kowane ɗan Nijeriya ya shigo a dama da shi a harkar tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa a maimakon barin hakan a hannun hukumomin tsaro.

Lagbaja wanda ya samu wakilcin Babban Hafsa mai kula da horaswa a rundunar, Manjo-Janar Sani Gambo Muhammad, ya ce ba abu ne mai yiyuwa ga jami’an tsaro miliyan 2 su iya tsare al’ummar Nijeriya fiye da mutum miliyan 200.

Babban hafsan sojan, wanda ya ce gwamnatin Nijeriya na da niyyar ɗaukar ƙarin sojoji kamar yadda ta yi alƙawari, ya jaddada cewa rundunar sojin ƙasar, da sauran hukumomin tsaro, na fama da ƙarancin dakaru.

Ya kuma bayyana matsalolin rashin wadatattun kuɗi da ma’aikata da kayan aiki da kuma gurguwar fahimtar da ‘yan Nijeriya suka yi wa harkar tsaro a matsayin abubuwan da ke tarnaki ga ayyukan rundunar.