An gargadi mazauna Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, su guji sayen ruwan leda da aka saka a kuloli bayan bata-gari sun sace wasu kuloli a asibitin masu cutar tarin fuka a lokacin zanga-zangar #EndSARS.
Kakakin asibitin, Ekeng Edet, ya shaida wa Aminiya cewa yawancin kulolin da bata-gari suka yi wasoson “an ajiye samfurin jinin masu fama da tarin fuka da cutar AIDS, amma suka zubar da samfurin suka yi awon gaba da robobin suna sayar wa jama’a”, inji shi.
Ya “shawarci masu sayen ruwan leda su guji sayen wanda aka sa cikin kula domin kada wani ya kamu da daya daga cikin cututtukan”.
Makonni biyun da suka wuce ne dai wasu masu zanga-zangar #EndSARS suka kutsa asibitin masu tarin fuka da karfin tsiya suka kwashe kulolin ajiyar samfurin jinin marasa lafiya.
Sun kuma far wa asibitin masu tabin hankali suka saki marasa lafiya suka kuma yi awon gaba gadajen kwanan marasa lafiya.
Duk da kurarin da Gwamantin Jihar Kuros Riba ta yi na bi gida-gida domin kwato kayan har yanzu wadanda suka dauke su sun ki dawo da su inda suka dauka ko mahadun hanya su ajiye kamar yadda gwamantin ta bukata.