✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A guji kokarin raba Najeriya – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso ya yi kira ga ‘yan Najeriya kan su mayar da hankulansu wajen abubuwan da za su hada kan…

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso ya yi kira ga ‘yan Najeriya kan su mayar da hankulansu wajen abubuwan da za su hada kan kasa a maimakon raba ta, duk kuwa da banbance-banbancen dake tsakaninsu.

Ya yi kiran ne a Ihitteafor-Ukwu na jihar Imo yayin bikin jana’izar mahaifin wani jagoran Kwankwasiyya a jihar, Mista Collins Onuoha.

“Abin sha’awa ne da alfahari yadda Allah ya albarkace mu da yaruka, addinai da al’adu daban-daban, wannan wani abu ne da ya kamata ya kara karfafa gwiwarmu ya kuma zama abin alfahari ga kowanne dan kasa,” inji shi.

Ya ce duk da yake Najeriya na fama da kalubale iri-iri, nasarorin da aka samu cikin shekaru 60 da samun ‘yancin kan kasar abin a yaba ne.

Kazalika, tsohon gwamnan ya ce hatta kasancewar kasar a doron dimokradiyya na tsawon shekaru 20 ba tare da kakkautawa ba abin a yaba ne.

Kwankwaso ya ce tsawon lokaci ya jima yana abota da yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya, inda ya ce zai ci gaba da aiki kafada da kafada da su wajen inganta rayuwarsu saboda muhimmancinsu.