Assalamu alaikum, yau zan yi magana kan yadda kayan masarufi suka yi tsada sanin kowane cewa yanzu talaka yana cikin wani hali, wanda babu abin da ya kamace shi sai addu’a, wadansu mutane abin da za su ci ma yana neman gagararsu, saboda tsada. Amma abin tambaya shi ne wa ya jefa mu cikin wannan hali? Amsar da mafi yawan ’yan Najeriya ke badawa ita ce shugabanni su ne suka saka talaka cikin wannan hali. Amma a nawa ra’ayin ba gwamnati kadai ya kamata a dora wa laifi ba kamata ya yi a raba laifin kamar haka.
1. TALAKAWA: Inda talaka yake da laifi shi ne rashin yi wa ita kanta gwamnatin addu’a idan ita gwamnati ta yi ba daidai ba, bai kamata mu rika zagin ta ba kamata ya yi mu yi mata adda’a Allah Ya ba su ikon yin daidai, amma mun tsaya sai zagi da muguwar addu’a, shi kuma Allah sai Ya bar mu da dabararmu.
2. ’YAN KASUWA: Ya kamata ’yan kasuwa ku ji tsoron Allah, ku sani mafi yawan matsalolin nan ku ne kuke jawo su da an yi magana za ku ce wai Dala ta tashi ko Saifa. Amma fa ku sani duk da kayan da kuka saya tun kafin Dala ta tashi, amma kun boye yanzu kuna saida wa talaka da tsada, wai domin kawai ku samu riba mai yawa. Kuma ku sani wannan babu wani abu da zai kare ku da shi a duniya da Lahira. Kamata ya yi ku ji tsoron Allah ku tausaya wa talaka, yanzu ma wani bala’in da ’yan kasuwar ke yi shi ne abincin da talaka zai iya saya mai sauki irin dangin masara ko gero da suka fara zuwa yanzu, sai, ’yan kasuwar su rika bin kasuwannin kauye suna sayewa suna boyewa, saboda ya kara tsada su fito da shi suna saida wa jama’a. Gaskiya wannan babban bala’i ne kuma wai irin wadannan mutanen da su ne ake zagin gwamnati kan wannan matsatsin da ake ciki muna fata za su ji kuma za su gyara.
GWAMNATI: Ita ma nan laifinta shi ne tana da yadda za ta yi ta ja wa wadansu birki amma ta ki, mun san babu wanda ya fi karfin doka.
Daga Idris Abubakar, Sabon Fegi, Talata Mafara, Jihar Zamfara, 09030280000
A taimaka wa masu gudun hijrah
Salam, Edita ka ba ni dama, domin yin kira ga masu hannu da shuni da ’yan kasuwa da gwamnatoci, su taimaka wajen tallafa wa mabukata da marasa shi da ’yan gudun hijrar Arewa maso Gabashin Najeriya da kayan Sallah kamar sutura da abinci da za su gudanar da bukukuwan Sallah kamar sauran jama’a. Kowa ya taimaki wani a lokacin da yake cikin bukatar taimako, shi ma Allah zai taimake shi a lokacin da yake da bukatar taimako.
Daga Kwamared Aminu dan Kaduna, Amanawa.
09035522212.
Zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari
Edita, bayan gaisuwa da fatan alheri, don Allah a ba ni dama in mika korafina ga Shugaban kasa. Ina so in jawo hankalin Shugaban kasa kan hanyoyinmu na kasa baki daya. Hanyoyin nan sun zama tarkon hada hadari, don haka suna bukatar dauki da gaggawa ta hanyar kafa dokar ta-baci. Shawara na ita ce don Allah duk kudaden da aka kwato kafin su soma fika-fiki a soma kashe su a kan hanyoyi da noma da ilimi da kiwon lafiya. Wannan ce canji da muke bida. Da haka rayukan talakawa zai inganta. Allah Ya taya ka riko.
Daga Moses John
Addu’a ya kamata mu yi ba korafi ba.
Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi tuni ga ’yan uwana ’yan Najeriya a kan su fahimci cewa addu’a ya kamata mu yi wa wannan gwamnatin ta Buhari ba korafi ba. An yi wa kasarmu barnar da gyaranta dole sai an dauki dogon lokaci. Kuma Baba yana iyaka kokarinsa. Don haka mu ma ’yan kasa idan muna bukatar ganin daidai dole kowa ya gyara inda ya san yana da matsala shi kuma Buhari mu yi masa addu’a.
Daga Shehu Mansur Sule Getso, Jihar Kano.
Ina wadanda suka kwakule idon yaron?
Don Allah Edita ka samar min wuri in yi tsokaci a kan yaron da aka kwakule wa idanu a Zariya wai Sarki da Gwamnan Jihar Kaduna sun dauki nauyin magani har ya warke, wannan shi ne a saki jaki a bugi taiki. Tambaya a nan ita ce, ina matsafan? Shugabanni ku ji tsoron Allah!
Daga Haruna Katsina.
Zuwa ga Gwamna Ganduje
Salam, Aminiyar amana ina so ku isar da sakona zuwa ga Gwamna Abdullahi Ganduje a kan goge sunan Kwankwasiya da yake son ya yi a Kano ba komai ba ne illa almubazaranci da kudi. Idan har ya goge a kan gini, ai ba zai zo cikin zuciyarmu ya goge ba. Insha Allah 2019 muna Kwankwasiya!
Daga Amira Mukhtar Ibrahim, Fatakwal, 07035779109
’Yan kasuwa a ji tsoron Allah!
Mu gyara kasuwancinmu mu daina hada shi da cewa wai canji ne, mu kyautata wa kanmu domin al’umma. A sa tsoron Allah a zuciya a yi gyara a a kasuwancin don neman tsira. Allah Ya sa mu dace.
Daga Jamilu Madawaki, Abuja, 08033121619
Kira ga shugabannin Najeriya
Edita, don Allah ka ba ni dama in yi kira ga shugabannin kasata a kan su dubi Allah su tausaya wa talakawa domin tsadar kayan abinci ta yi yawa, kullum sai kara shiga cikin matsala ake yi. Allah Yana ganinku, kuma za mu hadu a gaban Allah.
Daga A. A. Gabari.
Game da kama dan Boko Haram
Kame wani dan Boko Haram da ke shirin shiga aikin soja da jami’an tsaro suka yi, ya nuna cewa jami’an suna da kwarewar da za su zakulo ’yan ta’adda a duk inda suka shiga, da fatan Allah Ya musu basira.
Daga Mahmud Salihu, kauran Namoda.
Ya kamata Najeriya ta yi koyi da Brazil
Salam Edita. Ina so ka ba ni dama domin in yi kira ga ’yan Majalisar Wakilai su yi koyi da kasar Brazil a kan tumbuke tsohuwar Shugabar kasarsu Misis Dilma Rousseff a kan Yakubu Dogara domin laifinsu iri daya ne, idan har muna so dimokuradiyyarmu ta yi armashi.
Daga A. Lawal K/kwaya, Katsina.
Jinjina ga Sarkin Kano
Salam. Abin da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi na fitowa fili ya bai wa Gwamnatin Tarayya shawara abin yabo ne. Dama haka ake zato ga malamai da iyayen kasa, koda yake kalamansa ba su yi wa wadansu dadi ba saboda tsabar son zuciya. Sun manta cewa ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Buhari a lokacin yakin neman zabe
Daga Nasir Albani, Bauchi.
Gaba dai Baba
Salam. Edita, ina neman alfarma a jaridarka domin jinjina ga Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan namijin kokarin da yake yi na gyara a kan shugabancin Babban Bankin kasa, saura a fara duba bangaren shari’a da sauran mukaman ’yan siyasa.
Daga Aminu Tanimu, Dakata.
Godiya ga Gwamnan Jigawa
Salam. Godiya ga Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar daya biya ma’aikata kudin hutu tare da fatan alheri ga dukkan al’ummar Najeriya