An bayyana cewa zai fi kyau a gaggauta magance rikice-rikicen da ke faruwa a shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF) ta yadda za a baiwa kowane bangare damar ci gaba da ayyukan bunkasa wasan kwallon kafa a Nijeriya.
Malam Mustapha Umar Tallo Gwarzo , wani kwararre a fannin horar da ‘yan wasan kwallon kafa shi ne ya bayyana haka a ganawarsa da Aminiya, inda ya ce lokaci ya yi da za a samu jituwar dukkanin bangarorin da suke rikici da juna domin tunkarar duk wani kalubale na wasan kwallon kafa a kasar nan.
Ya ce idan aka samu fahimtar juna ko shakka babu kasar nan za ta yi fice a fannin wasan kwallon kafa, sannan za ta zamo tauraruwa a Nahiyar Afirka da kuma duniya baki daya idan aka dubi irin yadda muke da ‘yan wasa masu matukar kwazo.
Mustapha Bello Gwarzo ya kuma yi kira ga ‘yan wasan dake bugawa kasar nan kwallo da su sanya kishin kasa a lokacin da suke kwallo kamar yadda ’yan kwallon wadansu kasashe ke nunawa.
Haka kuma ya yi amfani da wannan dama inda ya shawarci hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasa ta sake baiwa Steben Keshi damar sake horar da kungiyar Super Eagles.
A gaggauta magance rikicin shugabancin Hukumar NFF – Mustapha Umar
An bayyana cewa zai fi kyau a gaggauta magance rikice-rikicen da ke faruwa a shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF) ta yadda…