Wata gamayyar kungiyar dattawan yankin Arewa maso Gabas mai fafutukar kawo zaman lafiya da cigaba ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta sallamar manyan hafsoshin tsaro.
Gamayyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Zanna Goni, ta kuma koka kan abun da ta kira tabarbarewar harkokin tsaro a Najeriya.
- Shugabannin arewa sun bukaci Buhari ya kori hafsoshin tsaro
- Lawan ya gayawa Buhari yadda zai kori hafsoshin tsaro
A cewarsu, “Muna sake jaddada bukatar zuba sabbin hannuwa da za su zo da sabbin manufofi wadanda za su kai ga sauya fasalin tsaron kasa.
“Mun fahimci yadda lamura suka kai matuka wajen tabarbarewa karkashin wadannan manyan hafososhin.
“Babu ko tantama yanzu kusan komai ya dagule a ilahirin kasa: kashe-kashen al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba daga ’yan bindiga, ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa yanzu sun zama ruwan dare.
“Hakan ya yi sanadiyyar jefa mutane cikin halin zaman dar-dar da rashin tabbas.
“Muna kira ga Shugaba Buhari da ya saurari koke-koken mafi yawan ’yan Najeriya ta hanyar sauya fasalin tsaron kasa domin inganta harkar.
“A matsayinmu na dattawa, ba zai yiwu mu yi shiru ba alhali lamarin na ci wa ’yan Najeriya tuwo a kwarya.
“Har yanzu mun kasa fahimtar dalilin Shugaban Kasa na ci gaba da aiki da wadannan manyan hafososhi ba duk da kiraye-kirayen da ake masa na sallamar su daga kusan kowane bangare.
“Muna tunatar da Mai Girma Shugaban Kasa cewa ’yan kasa sun gaji da gafara sa a harkar tsaro amma har yanzu ba su ga kaho ba; Suna bukatar gani a kasa,” inji dattawan.
An dai jima ana kira ga Shugaba Buhari da ya sallami manyan hafsoshin ko za a samu sa’ida kan matsalar tsaron da ke kara ta’azzara kusan a kullum amma shugaban bai sauya su ba.
Hatta Majalisar Tarayya sai da ta bukaci shugaban da ya yi hakan, amma ya ki.