✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gaggauta kawo karshen rikicin Sudan — MDD

A tashi a farga kafin rikicin ya rikide zuwa yaki.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna a Sudan da su gaggauta dakatar da fadan, kafin rikicin ya rikide zuwa yaki.

Da yake magana a Kenya, Mista Guterres ya ce al’ummar Sudan na fuskantar bala’in jin kai, inda aka lalata asibitoci, an wawushe kayan abinci, yayin da miliyoyin mutane ke fuskantar karancin abinci.

Tun da farko, babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, wanda ke Sudan, ya ce yana kokarin samun kowane bangare don ba da damar kai kayayyakin jin kai zuwa yankunan da lamarin ya fi kamari.

Bangarori a Sudan sun amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki bakwai da za ta fara daga ranar Alhamis, amma tsagaita wutar da aka yi a baya ta wargaje.

Mista Griffiths ya ce an yi awon gaba da manyan motoci shida na Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a kan hanyarsu ta zuwa yankin Darfur mai fama da rikici, duk kuwa da tabbacin da aka yi musu na cewa za su tsira.