✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A gaggauta ceto daliban Islamiyyar Tegina —Buhari

Buhari ya ba da umarni a gaggauta kubutar da daliban Islamiyyar Tegina cikin koshin lafiya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron Najeriya da su kara kaimi su kubutar da daliban makarantar Islamiyya da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Tegina na Jihar Neja.

Buhari ya yi tir da sace daliban da aka yi, ya kuma ba da umarni a gaggauta gano maboyar masu garkuwa da su a kuma ceto yaran cikin koshin lafiya.

  1. ’Yan ina-da-kisa sun hallaka shugaban hukumar NECO
  2. ‘Shan sigari kan hallaka ’yan Najeriya 29,472 a kowacce shekara’

Wasu rahotanni na nuni da cewa wadanda suka jagoranci sace daliban Jangebe a Jihar Zamfara ne suka yi garkuwa da daliban Islamiyyar na Jihar Neja.

A ranar Lahadi ne gungun wasu ’yan bindiga suka farmaki Islmaiyyar da ke garin Tegina, inda suka yi awon gaba da su yayin da suke tsaka da karatu.

Sai dai gwamnatin Jihar Neja, ta hannun Mataimakin Gwamnan Jihar, Ahmed Mohammed Ketso ta ce tana yin dukkan abin da ya dace wajen ceto daliban kamar yadda ta yi wajen kubutar da Daliban Kagara.