✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A fara duba watan Ramadan daga ranar Litinin —Sarkin Musulmi

Ranar dai ita ce ta yi daidai da 29 ga Sha'aban na shekarar 1442 bayan Hijira.

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ba da umarnin fara duba jinjirin watan Ramadan daga ranar Litinin 12 ga watan Afirilu 2021.

Ranar dai ita ce ta yi daidai da 29 ga Sha’aban na shekarar 1442 bayan Hijira.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a takardar da shugaban Kwamitin Ganin Wata na majalisar Sarkin Musulmi kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid  ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce duk wanda ya ga watan zai iya sanar da Hakimi ko uban kasar da yake kusa da shi domin sanar da Fadar Sarkin Musulmin.

Sanarwar ta kuma bayar da lambobin da za a  iya kira domin sanar da kwamitin ganin wata kamar haka: 08037157100, 07067416900, 08036149757, 08035965322.