A ranar Juma’a Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta ba da umarnin a garkame Abdulrasheed Maina a gidan Maza har zuwa lokacin da za a kammala shari’arsa.
Alkalin da ya jagorancin zaman kotun, Mai Shari’a Okong Abang ne ya bayar da umarnin, bayan shawarar bukatar hakan da lauyan Hukumar EFCC, Muhammad Abubakar ya gabatar.
Abdulrasheed Maina, wanda shi ne tsohon Shugaban Kwamitin yi wa tsarin fansho na kasa garambawul, yana fuskantar tuhuma ta almundahanar kimanin naira biliyan biyu da Hukumar EFCC ke yi masa.
Aminiya ta ruwaito cewa a wannan makon ne aka damko Abdulrasheed Maina a birnin Niamey na Jamhuriyyar Nijar, bayan an dauki tsawon lokaci ana nemansa sakamakon tsallake belin da ya yi, lamarin da ya kai ga an cafke Sanata Ali Ndume da ya tsaya masa a matsayin jingina.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito kotun ta bayar da belin Sanata Ndume bayan ya shafe kwanaki biyar a tsare sakamakon gaza gabatar mata da Maina a lokuta da dama da ta bukata.
Maina ya halarci zaman kotun na karshe a watan Yuli, inda ya yi layar zana har karo shida a jerin zaman da ta gudanar tun daga ranar 29 ga watan Satumba.