Shugabannin yankin Kudu maso Gabas a Najeriya sun yi kira ga matasa da su dakatar da zanga-zangar #EndSARS da suke gudanarwa.
A taron gwamnonin, ’Yan Majaliar Tarayya da sauran shugabannin kabilar Igbo, sun ce dakatar da zanga-zangar ta zama wajibi saboda yadda bata-gari suka shiga ciki suna aikata ta’asa da kuma tayar da hankula.
- #EndSARS: Ba za mu zura wa mabarnata ido ba —Buhari
- Sultan ya roki limaman Juma’a su yi hudubar zaman lafiya
“Muna jajanta wa Gwamnatin Jihar Legas da sauran jihohi bisa asarar rayuka da aka yi a zanga-zangar.
“Muna rokon matasan kasar nan da su dakatar da zanga-zangar da yanzu ’yan daba duka kwace”, inji taron shugabannin yankin.
Da yake kira da a zauna lafiya tsakanin kabilun Nijeriya, shugaban kungiyar, Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gano wadanda harbin da aka yi a taron masu zangar #EndSARS ya ritsa da su a Jihar Legas don bi musu hakkinsu.
Kazalika ya yi Allah-wadai da wani bidiyon shugaban kungiyar ’yan awaren Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da ke yawo a shafukan sada zumunta.
Shugabannin na Gabas sun ce Nnamdi Kanu na yi watsi da bidiyon, inda suke yi kira ga gwamnoni da su dauki matakana kare al’umma a jihohinsu.
Umahi ya kuma shawarci gwamnoni da su jawo matasa kusa da gwamnati domin su bayar da tasu gudunmawar.
Ya kuma ba wa matasa hakuri cewa yi wa shugabanni afuwa a inda suka yi kuskure a shugabancinsu.