Majalisar Koli ta Musulunci a Najeriya, NSCIA karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ta nemi a dakatar da masu shiga I’tikafi a lokacin watan Azumin bana.
Sanarwar da Majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce matakin hakan na zuwa saboda yadda har yanzu annobar Coronavirus ke ci gaba da cin kasuwarta.
- Gwamnati ta kara wa’adin hutun dalibai a Kano
- PSG ta sanya sharadin sayen Ronaldo
- An bai wa Zulum lambar yabo a Jami’ar Ibadan
Majalisar tana kuma kira ga al’ummar musulmi da su yi wa kawunansu karatun ta nutsu wajen kiyaye matakan dakile yaduwar cutar Coronavirus yayin gudanar da ibadunsu a watan azumin na bana.
Bayan taya al’ummar Musulmi murnar gabatowar watan Azumin na bana, tana kuma gargadin da a rika kauracewa shiga taron jama’a ta hanyar bayar da tazara.
Aminiya ta ruwaito Sarkin Musulmin yana ba da umarnin fara duba jinjirin watan Ramadan daga ranar Litinin, 12 ga watan Afrilun 2021.
Ranar dai ita ce za ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban na shekarar 1442 bayan Hijira.