Kimanin mako biyu da suka wuce ne a ranar 27 ga Fabrairun 2018 Majalisar Dokoki ta Jihar Kwara ta zartar da kudurin dokar da ta hana a rika ba tsofaffin gwamnoni da mataimakansu da kuma wadanda suka taba rike mukaman siyasa kudin sallama idan sun kammala wa’adin mulki. An zartar da kudurin dokar ce bayan da kwamitin da ke kula da dauka da kuma sallamar ma’aikata na majalisar ya yi nazari game da dokar.
Gwamnonin jihohin kasar nan kan kashe biliyoyin Naira wajen biyan fansho ga tsofaffin gwamnoni wadanda kuma sanatoci ne masu ci ko ministoci da suke karbar alabashi daga dukiyar kasa. Tsofaffin gwamnoni 21 da mataimakansu yanzu haka suna aiki a matsayin ko dai sanatoci ko ministoci.
Majalisun dokoki na jihohi da dama sun amince da dimbin kudaden sallama ga tsofaffin gwmnonin da mataimakansu. Alal misali, a Jihar Legas dokar biyan fansho ta shekarar 2007 ta amince a ba tsohon Gwamna gidajen alfarma guda biyu, daya a Legas daya kuma a Abuja da zai zauna tare da iyalinsa har tsawon rayuwarsa. Sannan za a saya masa manyan motoci guda 6 da za a rika canja masa su a duk bayan shekara 3, sannan dokar ta amince a rika ba tsohon Gwamnan alawus din kashi 300 na albashin da yake karba a shekara, kuma za a rika biyansa ne a duk bayan shekara 2, sannan an amince wa Gwamnan ya ziyarci duk irin asibitin da yake so a duba lafiyarsa da ta iyalinsa kyauta har na tsawon rayuwarsa. Sannan za a rika ba tsohon Gwamnan wasu alawus na kula da gida da na biyan ma’aikatan da ke masa aiki a gida.
A Jihar Ribas kuwa, an amince tsohon Gwamna ya rika karbar kashi 10 daga cikin 100 na albashinsa a shekara, sannan za a saya masa katafaren gida a duk inda yake so, ba ya ga manyan motoci uku da za a rika canja masa a duk bayan shekara 3.
A Jihar Akwa Ibom kuwa, tsohon Gwamna zai rika karbar fansho ne da yawansa ya kai albashin Gwamna mai ci har tsawon rayuwa. Sannan za a kula da lafiyarsa da ta iyalinsa kyauta muddin kudin ba su wuce Naira miliyan 100 a shekara ba. Sauran hakkokin da tsohon Gwamnan zai ci gajiyarsu a Jihar Akwa Ibom sun hada da samar masa da masu hidima a gida da suka hada da masu dafa masa abinci da direbobi da masu gadinsa.
A Jihar Kano, dokar fansho ta tsofaffin gwamnoni da mataimakansu ta 2007 ta nuna Gwamna zai rika karbar albashin kashi 100 bisa 100 ne a matsayin kudin fansho tare da mataimakinsa. Kuma tsohon Gwamna da Mataimakinsa a Kano za su ci gajiyar kula da lafiyarsu kyauta da ta iyalinsu. Sannan suna da damar tafiya hutun kwana uku a shekara a duk inda suke so walau a Najeriya ko a kasar waje.
A Jihar Gombe, dokar biyan fansho ta tsofaffin gwamnoni da mataimakinsu ta nuna ana ba tsohon Gwamna ne zunzurutun Naira miliyan 300 a matsayin kudin fansho. A Jihar Zamfara, dokar biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu ta fansho ta 2006 ta nuna za a rika ba tsohon Gwamna da mataimakinsa motocin hawa na alfarma guda biyu duk bayan shekara 4 baya ga kula da kiwon lafiyarsu da ta iyalinsu kyauta walau a wajen kasa ne ko a Najeriya. Sannan za a ba su gidaje masu dakunan kwana hur-hudu da ofis da wayoyin sadarwa kyauta da kuma biya musu kudin tafiya yin hutu na tsawon kwana 30 a Najeriya ko a wata kasa.
Dokar da ke kula da da’ar Ma’aikata a sashe na 2 (a) ta nuna bai dace ma’aikaci ya rika karbar albashi ko alawus sau biyu a lokaci guda ba. Sannan dokar da ke kula da masu rike da mukaman siyasa mai lamba 14 (a) ba ta amince dan majalisa ya rika karbar kudi a matsayin albashi ko fansho a wurin da ya yi aiki a baya ba alhali yana karbar albashi a majalisa ba. Don haka dokar ta nuna ba daidai ba ne mutum ya rika karbar fensho sau biyu a lokaci daya.
Bai dace ma’aikaci ya rika karbar kudin sallama sau biyu a lokaci guda daga asusun gwamnati ba. Akwai bukatar a yi wa duk dokar da ta amince da irin haka kwaskwarima, don doka ce da ta fifita wani bangare fiye da wani a harkar aikin gwamnati.
Maganar gaskiya ba daidai ba ne yadda ake biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu makudan kudi a matsayin kudin sallama yayin da ake ba sauran ma’aikatan da suka yi ritaya cikin cokali.
Don haka akwai bukatar Hukumar Kula da da’ar Ma’aikata ta yi dokar hana duk wani tsohon Gwamna da mataimakinsa karbar kudin fansho a duk lokacin da suke rike da mukaman sanata ko minista. Wannan ke sa galibin jihohin ba su iya biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 18 da dan fanshon da bai taka kara ya karya ba ga ma’aikata. Dokar za ta kawo sauki ga jihohin da suke fama da karancin kudi duk da dimbin tallafin da Gwamnatin Tarayya ta rika ba su don su biya albashi da hakkokin ma’aikatanasu. Matakin da Majalisar Dokoki ta Jihar Kwara suka dauka na hana biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho abin yabawa ne. Kuma muna kira ga sauran jihohi su bi sahu don hana duk wani tsohon Gwamna ko Mataimakinsa da ya zama sanata ko minista ci gaba da karbar fansho ta wajen gyara irin wadannan dokoki.