Kungiyoyin kare hakkin Bil’Adama (CSOs), sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauya dokar da ta tilasta sanya jami’in tsaro su shugabanci hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC).
Shugaban kungiyar Transparency Advocacy for Development Initiative (TADI), Yomi David, ya yi kiran a Abuja, inda ya ce sauya dokar kafa EFCC ne kadai zai kawo nasara a kudirin Buhari na yakar rashawa a Najeriya.
Ya yi kira ga Shugaban Kasar da ya gaggauta umurtar Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya sauya dokokin kafa EFCC na 2003, musamman wadda ta ce, “Dole a damka shugabancin hukumar a hannun jami’in tsaro (tsoho ko mai ci).
“Ya kamata Shugaba Buhari ya hana ’yan sanda da gurbatattun ’yan siyasa mulkar hukumar.
“Ya kawo kwararru masu ilimin bincike na karni na 21, wadanda suka yi zarra kan fasahar binciken kadarori da gano su, da kwato su da binciken masu laifi da kuma kwarewa wajen gurfanar da barayi a kotu.
“Muna rokon Shugaban Kasa ya aiwatar da shawarwarinmu domin ya tabbatar da cewa a shirye yake ya gyara hukumar” inji shi.
Ya ce hakan shi zai ba mutane kwararru, masu gaskiya, marasa tabo damar shugabantar hukumar.