✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A cikin wata 5 an kashe Fulani 325, an sace shanunsu dubu 15 – Miyyeti Allah

Alhaji Sale Bayare shi ne Babban Sakataren kungiyar Miyyeti Allah ta kasa a tattaunawarsa da ’yan jarida a Kaduna ya bayyana irin matsalolin da jama’ar…

Alhaji Sale Bayare shi ne Babban Sakataren kungiyar Miyyeti Allah ta kasa a tattaunawarsa da ’yan jarida a Kaduna ya bayyana irin matsalolin da jama’ar Fulani ke fuskanta a kasar nan inda ya ce Fulani ba masu son tashin hankali ba ne.

Aminiya– Mene ne makasudin wannan taron manema labarai?
Bayare: Akwai abubuwan da suke tada hankali da masifa da suke faruwa ga mu Fulanin Najeriya musamman masu kiwo yadda manoma da sauran al’umma suka sanya Fulani da makiyaya a gaba. Muna kuma ganin tunda ’yan jarida ba a can daji suke ba kuma cikin Fulanin nan ba ’ya’ya ne suke da su ’yan jarida ko alkalai ko sojoji ko ’yan sanda ko ’yan boko ba, sai ya zama abubuwan da suke faruwa ga Fulani kashi biyar cikin 100 ba a sani. Idan Bafulatani bai kare kansa da dabbobinsa da ’ya’yansa da zuriyarsa ba, gaba daya za a kawar da su daga bayan kasa. Idan kuma ya tashi kare kansa daya daga cikin wadanda suka kawo masa hari ya mutu sai ka ji an ce wai Fulani ’yan jihadi ko Fulani ’yan ta’adda sun yi kisa duk duniya sai a fada musu. Ana ganin kamar mu wadansu mutane ne da kawai duk lokacin da muka ga dama sai mu dauki makami mu kashe mutane.
Muna shaida wa duniya cewa cikin wata biyar kawai da suka wuce an kashe mana mutane kamar haka; a Jihar Nasarawa mun rasa mutum 125, a Jihar Kaduna a rikicin da aka yi a Kauru mun rasa mutum 12. A Jihar Benuwai kwanan nan a tsakanin kauyen Agatu da Guma da Logo mun rasa mutum 66. A Kwara a Asa da Moro da Pategi mun rasa mutum 46, a Taraba a karamar Hukumar Ibbi kawai mutanen da suke shigo mana daga bangaren Jihar Filato suna satar mana shanu sun kashe mana Fulani 17. A Filato cikin wannan lokaci, hade da rikicin Wase da Mangu da Barikin Ladi da Riyom mun rasa mutum 87.  Jimmilla a cikin wata biyar mun rasa mutum 325 kuma mun yi asarar shanu fiye da dubu 15.
Sannan mako biyu da suka wuce a kauyen Agasha da ke karamar Hukumar Goma a Jihar Benuwai sarki n garin da ake kira Tero Agasha ya gayyaci Fulani bakwai, dattawa uku da matasa hudu kan su je a tattauna yadda za a samu zama lafiya. A gabansa aka kama Fulanin nan aka yi musu yankan rago, aka kwashe gawarwakin zuwa hedikwatar ’yan sanda daga nan aka kai dakin ajiye gawa na asibiti, washegari Juma’a aka binne su.  A lokacin da ake binne su ’yan jarida da sauran jama’a na wurin, in ba don jaridar Daily Trust ba, babu wanda zai ji labarin. Saboda ba sa son duniya ta san ta’adin da ake yi mana. Har yanzu gwamnati da manyan jami’anta fushi suke yi a kan yaya aka yi labarin ya fita a jarida.
Ganin haka ne sai muka ziyarci Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar a nan Kaduna don shaida masa irin asarar rayuka da dukiyar da muka yi a cikin wata biyar da suka wuce.
Aminiya: A inda ake rigingimun hari ake kai muku ko a rikici ake kashe muku mutane?
Bayare: Kamar yadda kuka sani wata biyar zuwa yanzu in maganar gona ce an riga an girbe. Saboda haka ba lokaci ne yanzu da za a ce barna mutanenmu ke yi ba, saboda a yanzu ko’ina ya bushe, ciyawa ma da shanun za su ci babu. Su kabilar Tibi taro suke yi da matasansu kan yadda za su far wa Fulani domin su samu naman shanu. Sauran kabilu kuma tunda harkar tsaro a kasar nan ta tabarbare wadanda ake ganin suna da arziki kuma ba su da gatar komai daga hukuma su ne Fulani, sai kawai su tashi su far musu su debi shanu su sayar, masu kiwon kanana su ajiye a gidajensu suna kiwo, manyan kuma a diba a motoci a kai duk inda za a kai. Kamar a Jihar Filato saboda wannan al’ada ta son a raba mu da shanu ya sa mayanka a yanzu a Filato babu Bafulatani ko Bahaushe ko daya. Kai, babu wani Musulmi ko daya a mayankar Jos.  Duk wanda ke yanka sa a wurin nan za ka ga ba Bafulatani ba ne ko bBahaushe. Saboda ba sa son Bafulatani ko Bahaushen da zai ga shanu ya ce kai wannan a bincika ko ta sata ce. Tunda misali Bafulatani ba zai kai saniya da ciki ya sayar ba.  Yanzu an mayar da shanunmu ganima ne, sai kawai a far wa Bafulatani a kashe shi da yaransa da matansa a akwashe masa shanu a tafi da su duk inda aka ga dama.
Aminiya:  A jihohin Filato da Kaduna ana zargin Fulani da kai hare-hare ga al’ummar yanki. Yaya gaskiyar maganar take?
Bayare: Idan kuka bi tarin abubuwan da suka faru a zaben shekarar 2011 akwai rigingimu da aka yi irin wannan, akwai mutanen da suke jira duk lokacin da doka ta fadi sai su kai wa Fulani hari ko a Filato abin da suke mana ke nan. Muna can dawa muna bin halaliyarmu muna kiwo amma ba mu san cewa akwai wadanda suke jirar doka ta fadi sau far mana ba. Irinsu sun tara matasa sun ba su makamai kafin ka ce kwabo an karkashe mana dabbobi da mutane. Har yanzun nan wadannan mutane da suka yi wa Fulani ta’asa an sun su, kuma ana ganinsu amma ba a yi komai ba, mutumin da baya da gida ko keke yanzu yana hawa motoci. Kuma Bafulatanin ya sani cewa wannan gida sun kwashe gida shanunsa, kuma ga hukuma ya fada mata amma ba ta cewa komai. Ka ga idan wani ya yi hakuri wani ba zai yi ba, idan mahaifi ya bar zancen da na iya ki. Idan dan ya yi hakuri jika na iya cewa ba zai yi hakuri ba saboda yana ganin wanda ya saci shanun kakanninsa ya yi dukiya. Saboda haka wani lokaci Fulaninmu idan suka ga haka, sai su ce za su je su karbo shanunsu daga nan sai rikici ya barke. Bayan sun talauta mu, ba mu da inda za mu je dan takin da shanun suka bari da za ka shuka ’yar masara sai su ce mu tashi in ba haka ba kuma a far mana. Idan kuma kuka tashi domin kare kanku sai a ce don me, saboda duniya ba ta ji abin da aka fara yi muku ba. Muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitoci domin su binciki abubuwan da ake yi wa Fulani a kasar nan. Idan har an tabbatar da babu inda aka taba Bafulatani kafin ya kai hari, za mu ba da goyon baya da taimako kan yadda za a hukunta duk Bafulatanin da ya aikata laifi saboda ya zama darasi ga saura.
Aminiya: Me za ka ce kan zargin da ake yi wa Fulani na yawan fashi da makami da suke yi a wasu sassan Arewa?
Bayare: A kasar nan babu wata kabila ko al’umma da za a ce ba za a iya samun masu laifi a cikinta ba. Kuma mun san cewa duk wuraren da ake yawan samun rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya da manoma za a samu laifuffuka suna habaka a wuraren, saboda duk al’ummar da aka bar ta ta fara shiga rikici har aka fara zubar da jini, doka ba za ta zama komai a wurinsu ba. Kuma saboda asarar da mutane suka yi, inda wasu suka rasa iyayensu, wasu ’ya’yansu, wasu matansu za a samu imani ya ragu a wajen
irin wadannan mutane. A irin wannan hali sai mutane su shiga take daukar doka, a ga fashe-fashe sun yi yawa. Misali Bafulatani na da shanu kamar 50 ko 100 an zo an auka masa an kwashe su an tafi da su, ya
dawo ba ya da saniya ko daya wani sai zuciyarsa ta gurbace ya shiga wani hali kamar ya zama barawo ko
dan fashi. Kuma idan rikice-rikice suka faru makamai sukan shiga hannun mutane, kuma idan akwai makamai a hannun mutane, babu yadda za ka hana aikata laifaffuka, kamar yadda yanzu ake gani a jihohin Zamfara da Kaduna da Filato.
Aminiya: A karshe mene ne sakonka ga su Fulani?
Bayare: To, ina son na mika godiyarmu ga Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, kan kokarin da yake yi na daukar dawainiyar kungiyar Miyetti Allah ta kasa. Babu shakka ya yi kokarin kawar da abubuwan da suka sanya aka yi shekara da shekaru ba a yi zaben shugabannin ungiyar ba. Sakona ga al’ummar Fulani musamman wakilan da za su je zaben wannan kungiya da za a gudanar nan ba da dadewa ba, shi ne su sani kungiyar Miyetti Allah ba kungiya ce ta siyasa ba.
Don haka su natsu su zabi mutanen da suka kamata wadanda da dadi ba dadi ana nan tare da su a cikin harkokin kungiyar.