✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A binciki Naira 4.2 na asusun ajiyar bai daya yanzu

Labarin da Majalisar kasa ta bankado makon da ya wuce na da tayar da hankali, jin cewsa shekara biyu da fara aiwatar da tsarin asusun…

Labarin da Majalisar kasa ta bankado makon da ya wuce na da tayar da hankali, jin cewsa shekara biyu da fara aiwatar da tsarin asusun ajiyar bai daya na TSA har yanzu ba a yi binciken kudi a kansa ba. Odita-Janar na Tarayya Mista Anthony Ayine (AuGF) ne ya bankado batun, lokacin da ya bayyana gaban kwamitin  gaugawa na Majalisar Wakilai, karkashin jagorancin dan m ajalisa Abubakar Nuhu, inda aka dora wa kwamitin alhakin bin kadin  yadda  shirin ya gudana tsawon shekara biyu da ta gabata. Odita-Janar ya kasa tabbatar da hakikanin kudin da aka tara a asusun, tunda har yanzu ofishinsa bai bi kadin binciken kimar tsarin ba. Tsarin asusun ajiyar bai daya na TSA an bullo da shi ne cikin shekarar 2015 daidai lokacin  da aka kaddamar da Gwmanatin Shugaba Muhammad Buhari. Mista Ayine ya nuna gazawar binciken kudin asusu “kuskure” ne daga ofishinsa.

Tsarin TSA na da manufar danganta daukacin asusun ajiyar bankuna ga Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati. Kuma yana karkkashin kulawar Babbban Bankin Najeriya. Tasirinsa na farko ya tabbatar da danganta asusun ajiyar bankuna ga gwamnati, duk kudin shiga da kudin  kashewar Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati za su daidaita bisa doron ayyukan da ake gudanarwa. Tsarin  Asusun ajiyar bai daya na TSA bankin Duniya ya bayar da shawar bullo da shi don tabbatar da managarcin tsarin hada-hadar kudi ga kasashen da ke da tsarin sarrafa kudi mara kyau, tamkar wadanda ake gudanarwa a asusun ajiya masu yawa mara kan gado a Ma’aikati da Hukumomin Gwamnati.

Kafin a bullo da shi, Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati na gudanar da dubban asusun ajiyar ban kuna, inda mafi yawansu hukumomi ba su da masaniya  a kai. Zuwa yanzu tsarin “TSA” ya daidaita al’amura ta yadda za a iya tarairayar kudin al’umma da ke shiga su fita daga lalita. Tuni aka tabbatar da tara Naira tiriliyan hudu da biliyan 200 da suka shiga asusun ajiyar bai daya na Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati daban-daban.

Sabanin yadda gwamnati mai ci ta jajirce kan yaki da cin hanci da rashawa, rashin cikakken binciken tsarin asusun ajiyar bai daya na TSA da ofishin Odita-Janar na Tarayya (AuGF) ya yi, ya haifar wa tsarin matsala. Bayanin da Odita-Janar ya yin a cewa kuskure ne kawai ba abin yarda ba ne.  Bisa la’akari da kimar dokar aiwatar da binciken kudi da ofishin Odita-Janar ke da karfin aiwatarwa, kin aiwatarwa tsawon shekara biyu na nan a matsayin laifi. An yarda cewa Ayine sabo ne a ofishin Odoita-Janar, to ya fara yi wa ofishinsa garambawul don tabbatar da cewa ma’aikatansa suna aiwatar da abin da ya cancanta su yi. Aikin Gwmanati a Najeriya tattare yake da al’amura masu rikitar da tunani, kamar yadda aka saba jin an sace dukiyar al’umma a fili karara. Sakacin da ake yi a tsarin shi ke haifar da kin sauke nauyin da ya rataya kan ma’aikata, har zuwa kan muhimmin al’amarin da ya shafi asusun ajiyar bai daya na TSA. Hakki ne dai da ya rataya akan Ayine ya warware wannan badakala da ta cukurkuda al’amura saboda tsananin muninsa.

A bayyane yake karara fasahar zamani ita ce jigo wajen aiwatar da tsarin asusun ajiyar bai daya na TSA. Don haka muna kira ga Odita-Janar ya horar da ma’aikatan ofishin dabarun fasahar sadarwar zamani da suke bukata wajen binciken wadannan dimbimn kudi da ke ajiye a asusun. Idan har ya zama dole, Ofishin Odita-Janar ya lalubo ’yan Najeriya kwararru da ke da kwarewar binciken kudi da za su aiwatar da binciken da ake bukata kan asusun ajiyar bai daya. Mun fahimci cewa kudirin dokar binciken kudi tana gaban Majalisar kasa tun zamanin Samuel Ukura, amma har yanzu ba a tabbatar da dokar aiwatar da shi ba. kudurin na bukatar ofishin Odita-Janar na Tarayya ya samu cin gashin kansa, ta yadda tsarin jan ragamarsa da hada-hadar kudi su ci gashin kansu don cimma bukatun ayyukan da suka rataya akansu. Idan kudirin zai taimaka wa ofishin da karfin ikon aiwatar da binciken kudi, to majalisar kasa ta yi hanzarta tabbatar da dokar amincewa da shi.

Sai dai game da asusun ajiyar bai daya muna bukatar ganin an aiwatar da binciken bin diddigin abin da ya gabata nan da nan don tabbatar da cewa ba a fake da wannan nakasun an cutar da kasar nan ba. Kwamitin majalisa ya kamata ya gindaya wwa Mista Ayine wa’adin lokacin da ya kamata ya gabatar da kundin rahoton binciken kudi kan tsarin asusun ajiyar bai daya, ta yadda kasar nan za ta tantance irin ci gaban da aka samu.