✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A bincika min yadda aka dawo da Maina bakin aiki- Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya bayar da umarni cewa Abdullahi Abdulrasheed Maina ya tattara ina-shi-ina-shi ya kama gabansa. Mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai,…

Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya bayar da umarni cewa Abdullahi Abdulrasheed Maina ya tattara ina-shi-ina-shi ya kama gabansa.

Mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ne sanar da hakan, inda ya ce shugaban kasar ya bayar da umarni da cewa a sallami tsohon shugaban kwamitin binciken kudaden fanshon, wanda ake zargi da almundahana da cin hanci da rashawa nan take.

Hakanan kuma, shugaba Buhari ya bada umarni a bincika yadda aka yi har aka dawo da Maina bakin aiki, har aka tura shi ma’aikatar harkokin cikin gida.

Idan ba a manta ba, jim kadan bayan sanar da cewa an tura Maina ma’aikatan harkokin cikin gida a matsayin babban sakatare, Hukumar EFCC ta fitar da sanarwa inda ta ce yana cikin wadande suke zargi da almundahana, da cin hanci da rashawa. Lamarin ya janyo cece-kuce tsakanin jama’a inda wasu ke ganin bai kamata a rika saka mutanen da ake zargi da cin hanci cikin gwamnatin da ke takama da yaki da cin hancin ba.