Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya bukaci Gwamantin Tarayya ta ayyana makiyaya dauke da makami masu karkashe mutane a kauyukan jiharsa a matasyin ‘yan ta’adda.
Ortom ya ce kiran ya zama wajibi saboda yawaitar hare-harensu na ba gaira ba dalii a sassan jihar a ‘yan watannin nan, domin doka ta hukunta su.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Terva Akase ya fitar ta ce ko a ranar Juma’a, ‘yan bindigar sun kashe mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama a kauyen Tse-Chembe na Karamar Hukumar Logo ta jihar.
Terva Akase wanda ya jaddada dokar jihar ta haramta yawo da dabbobi ya yi tir da hare-haren tare da cewa babu wanda zai saba dokar ya kuma rika zubar da jinin mutane sai ‘yan ta’adda.
Ortom wanda ya yaba wa sojojin rundunar Operation Whirl Stroke bisa daukinda suka kai wa jama’ar Tse-Chembe a kan kari, ya ce ayyana mabarnatan a matsayin ‘yan ta’adda zai ba wa jama’ar yankunan da abin ya shafa kwarin gwiwar kai rahoton duk wanda ba su yarda da motsinsa ba.