Ministan Ayyuka, Injiniya Dave Umahi, ya ce a wata mai zuwa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da aikin gina latafaren titi daga Sakkwato zuwa Badagry da ke Jihar Legas.
Umahi ya ce a wata mai zuwa Shugaba Tinubu zai kaddamar da aikin titin mai tsawo kilomita 1,000 a Jihar Kebbi.
Da yake tattaunawa a Jihar Kebbi da masu ruwa da tsaki kan rukunin farko da na biyu na aikin jihohin Kebbi da Sakkwato, Umahi ya shaida musu cewa aikin zai fara ne daga bangaren da ke da nisa kilomita 258 a jihar.
Ya kara da cewa titin yana daga cikin aiki gina titin Trans-Sahara da zai hada Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
- Matan sojoji sun tallafa wa gidajen marayu a Borno
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ake Kara Wa ‘Yan ‘Band A’ Kuɗin Wutar Lantarki
Ministan ya ce san shafe shekaru 48 ana magana a kan gina titin domin bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da sauran kasashen Afirka, amma ba a yi ba sai da Tinubu ya hau mulki.
Da yake jawabi, Gwamna Nasiru Idris, ya ce batun aikin titin ya faranta wa al’ummar jihar rai.
Ya kara da cewa gina titin zai kawo saukin rayuwa da kuma taimakawa wajen domin cimma burin ’yan kasa da dama.